Sarkin Musulmi: Dole a fada mana inda kudin satar da Gwamnatin Buhari ta karbo suke shiga

Sarkin Musulmi: Dole a fada mana inda kudin satar da Gwamnatin Buhari ta karbo suke shiga

- Sarkin Musulmi yana so ayi karin-haske kan kudin satar da ake ikirarin karbewa

- Sultan ya ce al’umma ta na bukatar gwamnatin tarayya ta fadi inda ake kai kudin

- Mai alfarma Saad Abubakar III yace ayi wa jama’a bayanin Biliyan nawa aka samu

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi karin-haske a game da kudin satar da ta ke karbowa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya na cewa ayi wa ‘Yan Najeriya bayanin abin da aka karbo, da inda aka kai kudin.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya yi wannan jawabi ne a garin Sokoto a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2021, yayin da yake magana a wajen wani taro.

KU KARANTA: Neman zaman lafiya shi ne a ba Mutanen Kudu kujerar Shugaban kasa

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya tare da hadin-kan hukumar ICPC ta shirya wannan zama da aka yi da masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso yamma.

Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, shi ne ya wakilci Sarkin Musulmi a wajen taron.

Farfesa Sambo Wali Junaidu a madadin Muhammadu Sa’ad Abubakar III yake cewa yin shiru a kan kudin da aka karbe daga hannun barayi, babbar matsala ce.

“Gwamnati ta na bin ‘yan Najeriya bashin bayani, muna so mu san biliyan nawa aka karbo daga hannun tsofaffin shugabannin da aka yi a baya.” Inji Sultan Sa’ad III.

Sarkin Musulmi: Dole a fada mana inda kudin satar da Gwamnatin Buhari ta karbo suke shiga
Shugaba Buhari, Sultan da sauran Sarakuna Hoto: @Abuja_facts
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga farkon shekara zuwa yau, Boko Haram ta kai hare-hare sama da 100

Jaridar National Accord ta rahoto Sultan ya na cewa: “Ina kudin suke, kuma me ake yi da su?”

“Bayanin ya na da muhimmanci, la’akari da halin da harkar ilmi da sauran abubuwan more rayuwa irinsu titunanmu suke ciki, suna bukatar gwamnati ta duba su.”

Sultan yake cewa Sarakunan Usmaniyya sun rubuta wasu littatafan musulunci da za su taimaka wajen yaki da sata da yadda za a bi wajen magance wannan matsalar.

Gidauniyar AbdulSamad Rabiu ta na kashe N40bn domin inganta harkar ilmi a Afrika a duk shekara, ana ware wasu makudan kudi, a ba jami'o'in da ke Najeriya.

Jami'ar UNIMAID da ke garin Maiduguri, jihar Borno, ta tabbatar da cewa shugaban kamfanin na BUA ya ba su gudumuwar N1bn domin su gina abubuwan more rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel