Majalisar Wakilai Na Duba Yiwuwar Soke Bautar Kasa ta NYSC Kwata-kwata a Najeriya

Majalisar Wakilai Na Duba Yiwuwar Soke Bautar Kasa ta NYSC Kwata-kwata a Najeriya

- Majalisar wakilai na ci gaba da zama kan kudurin da ke neman soke Bautar Kasa a Najeriya

- Majalisar tuni ta yi zama na biyu kan yunkurin, wanda da alamu akwai hujjoji masu kyau

- An koka kan yadda lamarin tsaro ya yi sanadiyyar lalata manufar kirkirar bautar kasa a Najeriya

Majalisar Wakilai na duba yiwuwar dakatar da shirin bautar Kasa na NYSC, jaridar Punch ta ruwaito.

Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na Canji shekarar 2020, wanda ke neman soke dokar NYSC, an gabatar da shi a karatu na biyu.

Wanda ya dauki nauyin yunkurin, Mista Awaji-Inombek Abiante, a cikin bayanin shawarar, ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC.

KU KARANTA: Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Majalisar Wakilai Na Duba Yiwuwar Dakatar Da Yin Bautan Kasa ta NYSC a Najeriya
Majalisar Wakilai Na Duba Yiwuwar Dakatar Da Yin Bautan Kasa ta NYSC a Najeriya Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wani bangare na cewa, “Wannan kudirin yana neman a soke Sashi na 315 (5) (a) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, 1999, (kamar yadda aka yi kwaskwarima) a kan wadannan dalilai:

“Kisan gilla ga mambobin bautan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a wasu sassan kasar saboda ta’addancin 'yan bindiga, tsattsauran ra’ayin addini da rikicin kabilanci; yawan sace-sacen mambobin bautar kasa da ake yi a fadin kasar;

“Hukumomi da ma’aikatu na gwamnati da masu zaman kansu sun daina daukar matasa kwararrun 'yan Najeriya aiki.

"Don haka sun dogara kacokan kan samuwar ‘yan yi wa kasa hidiman da ba a biyansu albashi mai tsoka kuma ake watsar da su ba tare da cimma komai ba a karshen shekarar su ba tare da fatan samun aiki ba;

“Saboda rashin tsaro a duk fadin kasa, yanzu haka hukumar kula da bautar kasa ta fara tura 'yan bautan kasa yankinsu, don haka ya saba daya daga cikin manufofin kafa kungiyar, watau bunkasa alakar da ke tsakanin matasan Najeriya da inganta kasa, hadin kai da hadewa.”

Hukumonin tsaro a Najeriya sun kuma ba da shawarin wuraren da ya kamata a kai 'yan bautan kasa da kuma yankunan da ke da hadurra da basu dace a kai su ba.

Gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon ta kafa NYSC ne a ranar 22 ga Mayu, 1973, a karkashin Doka mai lamba 24 ta 1973 a matsayin hanyar sasantawa da sake hada kan ‘yan Najeriya bayan yakin basasa tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Janairun 1970.

KU KARANTA: Matar Osinbajo Ta Kai Ta'aziyya Gidan Marigayi Janar Attahiru, Da Sauran Jami'ai

A wani labarin, Kwamitin Jagorancin Shugaban Kasa (PSC) kan cutar Korona ya fitar da sunayen matafiya 90 da ya ayyana a matsayin ‘Mutanen da ake nema, saboda gujewa kebewar kwanaki bakwai, PM News ta ruwaito.

Kebewa ya zama tilas ga mutanen da suka zo daga kasashe masu tsanani, kamar su Brazil, Indiya da Turkiya, inda ake da yawaitar cutar Korona.

Shugaban kwamitin kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce wadanda suka yi kuskuren sun hada da ’yan Najeriya 63 da 'yan kasashen waje 27.

Asali: Legit.ng

Online view pixel