Wabba: El-Rufai Ya Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50 Su Fatattaki NLC

Wabba: El-Rufai Ya Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50 Su Fatattaki NLC

- Kungiyar kwadago ta NLC ta ce ba za ta saurara ba sam har sai ta kammala zanga-zangar kwanaki biyar

- Kungiyoyin kwadagon sun yi zargin cewa, akwai yiyuwar 'yan daba su fatattakesu yayin zanga-zangar

- A cewar Ayuba Wamba, gwamna El-Rufai ya yi hayar 'yan daba domin su tarwarsu yayin zanga-zanga

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ayuba Wabba, ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da yin hayar 'yan daba cike da manyan motoci 50 domin su fatattaki ma'aikata masu zanga-zanga a jihar.

Wabba ya bayyana hakan ne da safiyar ranar Laraba, 18 ga watan Mayu yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, a shirin Sunrise Daily.

Wabba ya zargin gwamnan jihar da biyan N500 ga kowane matashi domin kawo hargitsi a in da ma'aikata ke zanga-zangar korar adadi mai yawa na ma'aikatan gwamnati da jihar ta yi a ranar Talata, 18 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC Na Sake Rantsuwar Aiki da Gaskiya Tsakani da Allah

Ayuba Wabba: Gwamnatin El-Rufai Ta Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50
Ayuba Wabba: Gwamnatin El-Rufai Ta Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A kalamansa: "Kamar yadda nake fada muku, da safiyar yau din nan, jami'an tsaro sun kasance a can tun tuni kuma sun (gwamnatin jihar Kaduna) yi hayar manyan motoci 50 cike da 'yan daba domin su yi kokarin mamaye ofishin jiha na NLC in da mutanenmu suka suka taru.

"Wannan shine dimokradiyya? Ko a karkashin mulkin soja, shugabannin kwadago, ba a take dokokin kwadago ba kamar yadda aka yi a yau.

"Jami'an tsaro na can, suna ta daukar hotuna, suna daukar komai, dukkan motocin, dukkan mutanen."

KU KARANTA: Kasar Saudiyya Za Ta Ba Afrika Tallafin Korona Har Dala Biliyan Daya

A wani labarin, Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) ta hannun shugabanta na kasa Kwamared Williams Akporeha sakatarenta Kwamared Afolabi Olawale, ta yi barazanar kulle Najeriya saboda “girman kan” Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Shugabannin kungiyar a cikin wata sanarwa sun ce NUPENG ta yi matukar bakin ciki game da tashin hankalin da ya faru yayin da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ke zanga-zangar lumana ta “mulkin kama-karya da danniya na Gwamna Nasir El-Rufai a Jihar Kaduna.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel