Ku Sake Shi Yanzu: Gwamnatin Buhari Ta Yi Allah Wadai Da Tsare Shugaban Kasar Mali
- Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da tsare shugaban kasar Mali da aka yi a makon nan
- Gwamnatin Najeriya ta ce dole ne a saki wadanda aka tsaren ba tare da wani sharadi ba
- Najeriya ta ce hakan zai haifar da rashin zaman lafiya da dawo da demokradiyya a kasar Mali
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta aika sako zuwa ga sojoji a kasar Mali. Sakon cikin sauki ya ce: Ku saki Shugaba Bah Ndaw da Firayim Minista Moctar Ouane.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen, Ferdinand Nwonye, kamar yadda rahoton Channels TV ya ruwaito.
FG ta ce sakin dole ne ya kasance ba tare da wani sharadi ba, jaridar Sun ta kara da cewa.
KU KARANTA: Gwamna Zulum Na Jihar Borno Ya Yi Garambawul Ga Kwamishinonsa
Sanarwar ta ce:
“Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi Allah wadai da kakkausar murya da tsare shugaban rikon kwarya Bah Ndaw da Firayim Minista Moctar Ouane na Mali.
“Rahotanni sun ce sojoji sun tsare manyan jami’an biyu na gwamnatin rikon kwarya ta Mali zuwa sansanin Kati da ke kusa da Babban Birnin, Bamako a ranar Litinin, 24 ga Mayu 2021.
"Matakin ba abin yarda bane kwata-kwata kuma zai iya kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya da jadawalin dawo da mulkin demokradiyyar Mali."
Ku tuna Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasar Mali na rikon kwarya, Bah N’Daw, da Firayim Ministan kasar Moctar Ouane, sojoji sun tsare su a ranar Litinin, 24 ga watan Mayu.
Kame jami’an gwamnatin rikon kwaryar kasar ya biyo bayan garambawul da majalisar ministoci ta yi a kasar da ke yankin kudu da hamadar Sahara watanni tara bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugabanta na baya.
Har ila yau, a watan Agustan 2020, firaminista na Mali, Boubou Cisse, da shugaban kasa, Ibrahim Boubacar Keita, wasu sojoji sun kame su.
KU KARANTA: Kada Ku Sare Saboda Mutuwar Janar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ta ce an yi kokarin lalata ofisoshinta biyu a cikin jihar, TheCable ta ruwaito.
Rikici ya barke a yankin Ile-Epo na Legas ranar Litinin, yayin da masu zanga-zanga suka yi tattaki zuwa ofishin ‘yan sanda da ke yankin kan zargin kisan wani mutum da aka ce shi dan acaba ne, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wani mazaunin garin, wanda ya zanta da NAN, ya yi zargin cewa babbar mota ce ta kashe mai babur din.
Asali: Legit.ng