Bayan Mutuwar COAS Attahiru, FG Ta Bayyana Ranar da Wasu Sabbin Jirgaen Yaƙi Zasu Iso Najeriya
- Gwamnan CBN ya bayyana cewa nan da yan watanni jiragen yaƙi 6 zasu iso Najeriya daga ƙasar Amurka
- Gwamnan yace wannan na daga cikin jirage 12 da gwamnatin tarayya tayi yarjejeniya da Amurka shekara uku da suka gabata
- Ya kuma shawarci yan bindiga da sauran masu tada zaune tsaye dasu gaggauta tuba su aje makaman su kafin jami'ai su riske su
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa Najeriya zata samu sabbin jiragen yaƙi 12 daga ƙasar Amurka, waɗanda zasu taimaka wajen yaƙar matsalar tsaro, kamar yadda the cable ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Jam’iyyar PDP Ta Caccaki APC Kan Ƙona Ofisoshin INEC, Tace Tarihi Ba Zai Mata Kyau Ba
Ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyi bayan fitowa daga wani taro a Abuja, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Emefiele, Wanda ya koka kan yanda rashin tsaro ya taɓa tattalin arziƙin ƙasa, yace zuwan jiragen na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Najeriya da Amurka shekara uku da suka gabata.
Yace: "Idan kana son tattalin arziƙi ya haɓaka, to yakasance akwai tsaro a ƙasa, amma kasan cewar muna cikin wannan yanayin, shiyasa tattalin arziƙin mu ke tangal-tangal."
"Shekaru uku da suka gabata, gwamnatin tarayya ta ƙulla yarjejeniya da ƙasar Amurka wanda ya ƙunshi sayar da makaman soji daga gwamnati zuwa gwamnati."
KARANTA ANAN: Taɓarɓarewar Tsaro: CUPP Ta Buƙaci Shugaba Buhari Yayi Murabus
"Daga cikin wannan yarjejeniya, muna tsammanin isowar jiragen yaƙi 12 da zasu taimaka mana wajen magance matsalar tsaron da muke fama da ita."
"Na samu labarin guda shida daga cikinsu zasu iso Najeriya cikin watan Yuli zuwa watan Augusta." inji gwamnan.
Gwamnan ya shawarci duk wani ɗan bindiga da ya gaggauta aje makamanshi yazo ya zama ɗaya daga cikin waɗanda zasu ci gajiyar bashin da CBN ke bayar wa.
A wani labarin kuma Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC
Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha , ya bayyana cewa sai an magance talauci a Najeriya sannan za'a samu tsaro.
Sanatan yace rashin adalci da Talauci sune suka haifar da duk wannan ƙalubalen tsaron da ƙasar take fama da shi.
Asali: Legit.ng