Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC

Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC

- Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana cewa sai an magance talauci a Najeriya sannan za'a samu tsaro

- Sanatan yace rashin adalci da Talauci sune suka haifar da duk wannan ƙalubalen tsaron da ƙasar take fama da shi

- Yace koda za'a siyo dukkan makaman duniya matuƙar akwai talauci da rashin adalci to ba za'a samu nasara ba

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace matuƙar ba'a magance talauci da rashin adalci a Najeriya ba, to babu wani makami da zai yi nasara a yaƙin da ake da rashin tsaro a ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Jami'an Tsaro Sun Cafke Yan Bindiga 37 Dake Shirin Kai Hari INEC da Ofshin Yan Sanda

Okorocha, wanda yayi jawabi a wajen taron shekara-shekara na 2021 NBA, mai taken "Rawar da mutane zasu iya takawa a gwamnatin Najeriya', yace akwai dangantaka tsakanin talauci da rashin adalci.

Sanatan ya kuma yi fatan Najeriya zata cigaba da kasance wa tsintsiya ɗaya duk kuwa da kiraye-kirayen a raba ƙasar da wasu keyi daga sassa daban-daban, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC
Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC Hoto: @realrochas
Asali: Twitter

Okorocha yace:

"Bai kamata mu cigaba da tunanin cewa Najeriya zata tarwatse ba, Najeriya babbar ƙasa ce kuma ba zata tarwatse ba, bada jimawa ba za'a haifi sabuwar Najeriya."

KARANTA ANAN: Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar

"Akwai talauci da rashin adalci a cikin Najeriya, kuma waɗannan abubuwa biyu suna da dangantaka da juna."

"Matukar ba'a magance rashin adalci da talauci ba, to ko da zaku siyo dukkan makaman duniya domin yaƙar matsalar tsaro, bana ganin za'a samu sakamako mai kyau."

A wani labarin kuma Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli, inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace mutuwar shugaban rundunar Soji da sauran jami'ai 10 ya ƙaro matsaloli a ƙasar nan, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Shugaban yace Allah ne kaɗai yasan da faruwar wannan lamarin, amma ya faru a lokacin da ƙasar ke cikin ƙalubalen tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel