Jam’iyyar PDP Ta Caccaki APC Kan Ƙona Ofisoshin INEC, Tace Tarihi Ba Zai Mata Kyau Ba
- Babbar jam'iyyar hamayya PDP tace har yanzun tana kan bakarta cewa APC na da hannu a hare-haren da ake kaiwa ofishin hukumar zaɓe
- PDP tace wannan duk wata maƙarƙashiya ce da shugabannin APC ke son kitsawa don su kawo tsaiko a zaɓen 2023
- Jam'iyyar tayi kira ga sufetan yan sanda na ƙasa da ya gayyaci shugabannin APC domin su amsa tambayoyi kan lamarin
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa tarihi ba zai wa jam'iyyar APC kyauba idan ta cigaba da ƙona ofisoshin hukumar zaɓe, INEC, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Wasu Ƴan Bindiga Sun Tuba, Sun Miƙa Makaman Su a Jihar Adamawa
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana haka a wani jawabi da aka yi wa take da "Har yanzun PDP na zargin APC nada hannu a ƙona ofisoshin INEC"
Hukumar zaɓe INEC tace waɗannan hare-haren da ake kaiwa ofisoshinta zasu iya kawo tsaiko ga zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Ta kuma roƙi sufetan yan sanda na ƙasa da ya sanya wa jam'iyyar APC ido.
Jawabin yace: "PDP na nan akan bakarta cewa APC na da hannu a wasu tashe-tashen hankula kamar ƙona ofisoshin INEC domin ta ƙirƙiri wata matsala ta gaggawa da zata sa a samu tsaiko wajen gudanar da zaɓen 2023."
"Jam'iyyar PDP na jawo hankulan yan Najeriya da su fahimci gazawar APC da shugabanninta, saboda sun kasa ɗaukar matakan da ya dace wajen kare kayayyakin zaɓe daga yan bindiga."
KARANTA ANAN: Jami'an Tsaro Sun Cafke Yan Bindiga 37 Dake Shirin Kai Hari INEC da Ofshin Yan Sanda
"Muna son APC ta san cewa, ranar 29 ga watan Mayu 2023 itace ranar da zata bar Ofis, kuma tarihi ba zai mata kyau ba duba da irin halin ƙunci da ta ƙaƙabawa yan Najeriya."
Jawabin ya cigaba da cewa:
"APC ta gurɓata kasar mu, ta buɗe kofa ga yan bindiga da yan ta'adda, ta mayad da ƙasar mu filin yaƙi da jana'iza."
"Muna kira ga sufetan yan sanda na ƙasa da ya gayyaci Shugabannin jam'iyyar APC domin su amsa tambayoyi a kan ƙona ofisoshin hukumar zaɓe."
A wani labarin kuma Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC
Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha , ya bayyana cewa sai an magance talauci a Najeriya sannan za'a samu tsaro.
Sanatan yace rashin adalci da Talauci sune suka haifar da duk wannan ƙalubalen tsaron da ƙasar take fama da shi.
Asali: Legit.ng