Badakalar Ibori: An Tura £4.2M da Aka Kwato Zuwa Jihar Delta, Akanta-Janar

Badakalar Ibori: An Tura £4.2M da Aka Kwato Zuwa Jihar Delta, Akanta-Janar

- Aknata-janar na trayya ya bayyana cewa, tuni gwamnati ta tura kudaden da aka dawo dasu Lanadan zuwa Delta

- Ya bayyana haka ne a martaninsa ga majalisar wakilai da tace ta ga gibi a wasu bayanan kudin kasar

- A baya majalisar ta nemi zama dashi domin ya bada cikakken bayani kan in da kudaden suka shiga

Akanta Janar na Tarayya, Mista Ahmed Idris ya bayyana cewa tuni har an kai kudaden da tsohon gwamnan ya wawure £4.2m ga gwamnatin jihar Delta, Vangaurd ta ruwaito.

Babban Akanta na tarayya, ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai.

Kwamitin na aiki ne kan "Kimantawa da matsayin duk wasu kadarorin da aka kwato wadanda za a iya dawo dasu da kuma ba za a iya ba daga 2002 zuwa 2020 da hukumomin Gwamnatin Tarayyar Najeriya suka yi don Ingantaccen Amfani da su".

KU KARANTA: Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake

Da dumi-dumi: An Tura £4.2m da Aka Dawo Dasu Najeriya Zuwa Jihar Delta, Akanta-Janar
Da dumi-dumi: An Tura £4.2m da Aka Dawo Dasu Najeriya Zuwa Jihar Delta, Akanta-Janar Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yana mayar da martani ne ga masu tsokaci cikin ‘yan majalisar kan banbancin dake tsakanin Tarayyar da kuma asusun hada hadar kudaden shiga na Tarayyar, da kuma rabewar kadarorin da aka kwato da kudaden.

Majalisar ta nemi ganawa da Akanta-Janar din a zamanta na ranar Litinin don yin bayani kan gibi da aka samu a bayanin da wakilinsa ya gabatarwa majalisar, in ji Daily Trust.

KU KARANTA: Kada Ku Sare Saboda Mutuwar Janar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya aiwatar da kwarya-kwaryar garambawul a cikin majalisarsa tare da sauya kwamishinoni uku, The Punch ta ruwaito.

Shawarwarin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata daga mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Danjuma Ali.

Ali ya ce an mayar da Kwamishiniyar Albarkatun Dabbobi da Bunkasa Kiwon Kifi, Juliana Bitrus zuwa Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Dan Adam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel