Gwamna Zulum Na Jihar Borno Ya Yi Garambawul Ga Kwamishinoninsa

Gwamna Zulum Na Jihar Borno Ya Yi Garambawul Ga Kwamishinoninsa

- Gwamnan jihar Borno, ya yi kwaskwarima ga majalisarsa, inda ya sauyawa wasu kwamishinoni wajajen aiki

- Rahoto ya bayyana dalla-dalla yadda gwamnan ya yi garambawul ga ma'aikatun jihar da kwamishinoninsa

- An kuma gano wata badakalar ma'aikatan kiwon lafiya na bogi a wasu sassa na ma'aikatar kiwon lafiya

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya aiwatar da kwarya-kwaryar garambawul a cikin majalisarsa tare da sauya kwamishinoni uku, The Punch ta ruwaito.

Shawarwarin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata daga mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Danjuma Ali.

Ali ya ce an mayar da Kwamishiniyar Albarkatun Dabbobi da Bunkasa Kiwon Kifi, Juliana Bitrus zuwa Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Dan Adam.

KU KARANTA: Badakalar Ibori: An Tura £4.2M da Aka Kwato Zuwa Jihar Delta, Akanta-Janar

Gwamna Zulum Na Jihar Borno Ya Yi Garambawul Ga Kwamishinonsa
Gwamna Zulum Na Jihar Borno Ya Yi Garambawul Ga Kwamishinonsa Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Kwamishinan Muhalli, Alhaji Lawan Walama, yanzu shi ne zai kula da Ma’aikatar Albarkatun Dabbobi da Bunkasa Kiwon Kifi.

Ali ya kuma bayyana cewa Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari'a, Alhaji Kaka-Shehu Lawan yana da karin aikin kula da Ma'aikatar Muhalli.

A wani labarin kuma, Zulum ya amince da sake kafa hukumar kula da cigaban kiwon lafiya matakin farko ta Borno tare da nada Ahmed Tijani a matsayin Shugaba.

Ali ya ce Zulum ya kuma amince da nadin Dakta Joseph Jatau a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Asibitocin Borno nan take da kuma Abubakar Suleiman a matsayin Mukaddashin Janar Manaja na Hukumar Kare Muhalli ta Borno.

A cewar Ali, gwamnan kamar yadda sashi na 9 karamin sashi na 1 na dokar hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta shekarar 2013, ya amince da nadin Dr Abba Goni a matsayin Darakta na Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a matakin farko ta jihar.

Wadannan sauye-sauye sun biyo bayan bakado wata badakalar ma'aikatan bogi da gwamnatin jihar ta Borno ta bankado.

KU KARANTA: Kada Ku Sare Saboda Mutuwar Janar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya

A wani labarin, Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya ce shi kadai ne gwamnan Najeriya da ba ya karbar albashi duk wata, PM News ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana cewa bayan an cire haraji daga albashinsa, sai ya tura ragowar kudin zuwa gidajen marasa galihu don kula da su.

Ya kara da cewa ya kasance yana yiwa jihar aiki ne.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Obiano ya bayyana hakan ne a mahaifarsa, Aguleri a karamar hukumar Anambra ta gabas a jihar ta Anambra jim kadan bayan ya duba fasinjojin kasa da kasa na Anambra da kuma tashar jirgin saman Cargo a Umueri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel