Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake

Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake

- Gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa, shi albashinsa na wata-wata bai rufe masa ido ba

- Ya bayyana cewa, yakan tallafawa marasa galihu ne da dukkan albashinsa na wata-wata kullum

- Hakazalika ya siffanta kansa da mutum mai kwarjini da kima a idon al'umma saboda aiki tukuru

Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya ce shi kadai ne gwamnan Najeriya da ba ya karbar albashi duk wata, PM News ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana cewa bayan an cire haraji daga albashinsa, sai ya tura ragowar kudin zuwa gidajen marasa galihu don kula da su.

Ya kara da cewa ya kasance yana yiwa jihar aiki ne.

KU KARANTA: An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa

Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake
Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Obiano ya bayyana hakan ne a mahaifarsa, Aguleri a karamar hukumar Anambra ta gabas a jihar ta Anambra jim kadan bayan ya duba fasinjojin kasa da kasa na Anambra da kuma tashar jirgin saman Cargo a Umueri.

Gwamnan wanda ya kuma bayyana kansa a matsayin "mutum ne mai kima da kwarjini," ya ce an gina filin jirgin saman da kyawawan wurare kamar yadda za a iya samu a kowane filin jirgin sama na duniya.

KU KARANTA: Jami'an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Kone Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kame 'Yan Ta'adda 12

A wani labarin, Kungiyar kasashen Musulmi (OIC) ta yaba wa gwamnatin Saudiyya kan kokarinta na tursasa Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare a Zirin Gaza, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito.

Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da mayakan Hamas ta ci gaba da aiki kwana uku a jere wanda ya kawo karshen rikicin kwanaki 11 da bangarorin biyu suka shafe suna yi.

SPA ya ce kungiyar OIC ta yaba wa Sarki Salman kan kalaman da ya yi a zantawarsa da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas cewa Saudiyya za ta ci gaba da bin matakan da suka dace domin matsin lamba ga Isra’ila ta dakatar da matakan da ta ke dauka da kuma hare-hare a birnin Kudus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: