Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishinan Sokoto, Tureta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Shafe Shekara 14 a Ofis

Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishinan Sokoto, Tureta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Shafe Shekara 14 a Ofis

- Kwamishinan Noma a jihar Sokoto, Alhaji Arziƙa Tureta, ya rigamu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya

- Tureta ya riƙe muƙamin kwamishina tun zamanin mulkin tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako.

- Marigayin ya rasu yana da shekara 62 a duniya, ya bar mata biyu tare da 'ya'ya bakwai

Kwamishin noma a jihar Sokoto, Alhaji Arziƙa Tureta, ya rigamu gidan gaskiya bayan shafe shekara 14 a ofis, kamar yadda the notion ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe

Tureta ya rasu ne yana da shekara 62 a duniya bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya.

Mai magana da yawun ma'aikatar noma, Muktar Dodo Iya, shine ya bayyanawa hukumar dillancin labarai (NAN) haka a Sokoto.

Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishin Sokoto, Tureta, Ya Rugamu Gidan Gaskiya Bayan Shafe Shekara 14 a Ofis
Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishin Sokoto, Tureta, Ya Rugamu Gidan Gaskiya Bayan Shafe Shekara 14 a Ofis Hoto: @thenstionnews
Asali: Twitter

Yace Alhaji Tureta ya rasu ne da sanyin safiyar yau Litinin a asibitin koyarwa na jami'ar Usman Ɗan-Fodio dake Sokoto (UDUS), ya rasu ya bar mata biyu da 'yaƴa bakwai.

KARANTA ANAN: Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

Yace marigayi Tureta ya taɓa riƙe kujearar ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Tureta a majalisar dokokin jihar Sokoto.

Daga baya ya zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Bodinga/DangeShuni/Tureta a majalisar wakilai ta tarayya

Hakanan kuma, Tureta yayi aiki a matsayin kwamishina a zamanin mulkin tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako, na tsawon shekara takwas.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya sake naɗa shi a matsayin kwamishinan noma, inda ya shafe shekara shida kafin rasuwarsa.

A halin yanzu, ana cigaba da shirye-shiryen gudanar da Jana'izarsa a mahaifarsa, Tureta, kamar yadda NAN ta ruwaito.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Fatattaki Yan Bindiga, Sun Kuɓutar da Mutanen da Suka Sace a Jihar Kaduna

Sojoji sun sami nasarar ƙuɓutar da wasu mutane da yan bindiga suka yi niyyar sace wa a ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kuɓutar da mutanen, yace mafi yawancin su matan aure ne.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel