Shugaba Buhari: Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli

Shugaba Buhari: Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli

- Shugaba Buhari yace mutuwar shugaban rundunar Soji da sauran jami'ai 10 ya ƙaro matsaloli a ƙasar nan

- Shugaban yace Allah ne kaɗai yasan da faruwar wannan lamarin, amma ya faru a lokacin da ƙasar ke cikin ƙalubalen tsaro

- Buhari yace zai cigaba da yin iya bakin kokarinsa wajen ganin ƙalubalen tsaro a Najeriya ya zama tarihi

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace rashin Janar Ibrahim Attahiru da manyan jami'ai 10 ya shafi yaƙin da ake da matsalar tsaro a ƙasar nan, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Sarki Salman Ya Kira Shugaba Buhari Ta Wayar Salula, Ya Masa Ta'aziyyar Mutuwar Janar Attahiru

Janar Attahiru tare da wasu jami'an soji sun rasa rayuwarsu ne ranar jumu'a a wani hatsarin jirgi da ya rutsa da su a Kaduna.

Shugaba Buhari: Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli
Shugaba Buhari: Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

A jawabin da shugaban yayi ranar Litinin lokacin da ya karɓi baƙuncin wakilan ƙungiyar gwamnoni (NGF) a fadarsa dake Abuja, yace zai cigaba da yin iya bakin kokarinsa wajen daƙile matsalar tsaron da ta addabi ƙasar nan.

Buhari yace:

"Wannan yanayi ne da Allah kaɗai yasan da faruwarsa, kuma ya faru a dai-dai lokacin da ƙalubalen tsaro ya zama muhimmin batun dake damun ƙasar nan."

"Kuma rashin zaɓaɓɓun jami'an mu ya ƙaro mana matsaloli, amma munsan halin da muke ciki kuma zamu cigaba da aiki tuƙuru, sannan muyi addu'a saboda Allah ya bamu ƙarfi da ƙwarin guiwar magance matsalolin."

KARANTA ANAN: Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

"Mutanen da suka zaɓe mu suna sane da alƙawurran da muka musu, duk da yanayin da muka tsinci kan mu a ciki zamu cigaba da yin iya bakin ƙoƙarin mu."

Da yake magana kan lamarin, shugaban ƙungiyar NGF, Kayode Fayemi, yace mutuwar gwarazan jami'an sojin ya maida hannun riga baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Fayemi ya kara da cewa duk da haka ya zama wajibi a yi nasara a yaƙin da ake da matsalar tsaro.

A wani.labarin kuma FG Ta Ɗauki Nauyin Ɗaliban Kwalejin Afaka da Aka Sace, Zata Canza Musu Wurin Zama Na Wucin Gadi

Gwamnatin tarayya ta gama shirin canza wa kwalejin FCFM wurin zama na wucin gadi biyo bayan sace ɗalibai da aka yi kwanakin baya a makarantar.

Gwamnatin ta kuma dauki nauyin biyawa ɗaliban da lamarin ya shafa kuɗin makaranta har su kammala karatun su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel