Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Bankawa Ofishin INEC Wuta a Enugu

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Bankawa Ofishin INEC Wuta a Enugu

- Yan bindiga sun banka wuta a ofishin hukumar zaɓe dake ƙaramar hukumar Igbo-Eze ta kudu, jihar Enugu

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kai ofishin ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Lahadi

- Wannan shine karo na uku da aka kai hari kuma aka ƙone ofishin INEC a jihar Enugu cikin wata ɗaya

Bayan makwanni biyu da ƙona hedkwatar hukumar zaɓe a jihar Enugu, wasu yan bindiga sun sake bankawa ofishin INEC wuta a yankin Igboeze ta kudu dake jihar.

KARANTA ANAN: Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun kai hari ofishin INEC dake garin Ibeagwa ranar Lahadi da daddare, inda maharan suka bankawa ofishin wuta da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Bankawa Ofishin INEC Wuta a Enugu
Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Bankawa Ofishin INEC Wuta a Enugu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

The nation ta ruwaito cewa wutar ta cigaba da ci a ɗaya daga cikin dakunan ofishin kafin hukumar kashe wutar jihar ta samu nasarar kashe ta.

Duk wani ƙoƙari na jin ta bakin kwashinan INEC na jihar, Dr. Emeka Ononamadu da kakakin hukumar INEC, Pius Eze, ya ci tura.

Amma shugaban hukumar kashe wuta na jihar Enugu, Engr. Okwudili Ohaa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

KARANRA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishinan Sokoto, Tureta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Shafe Shekara 14 a Ofis

Ohaa yace: "Mun samu rahoton ɓarkewar wuta a ofishin INEC dake Ibeagwa ƙaramar hukumar Igbo-Eze jiya da daddare."

"Mun yi ƙoƙarin zuwa wajen da gaggawa, kuma mun shawo kan lamarin, an samu nasarar kashe wutar baki ɗaya."

Ohaa ya ƙara da cewa ɗaki ɗaya ne kacal wutar ta shafa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wannan harin shine na uku da aka kai ofishin INEC kuma aka cinna wuta a jihar Enugu cikin wata ɗaya.

A wani labarin kuma Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da yin artabu da yan bindiga a ƙauyen Magami dake jihar Zamfara Ranar Asabar.

Kakakin hukumar yan sandan yace an kashe musu jami'ai biyu sakamakon lamarin, yayin da yan bindiga da yawan gaske suka baƙunci lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262