Matar Osinbajo Ta Kai Ta'aziyya Gidan Marigayi Janar Attahiru, Da Sauran Jami'ai

Matar Osinbajo Ta Kai Ta'aziyya Gidan Marigayi Janar Attahiru, Da Sauran Jami'ai

- Matar mataimakin shugaban kasa ta ziyarci mata da sauran iyalan marigayi Janar Attahiru

- Rahoto ya ce ta kuma ziyarci iyalan sauran jami'an da Najeriya ta rasa a hadarin na jirgin sama

- Ta taya su jaje tare da jimamin babban rashin da suka yi, kuma Najeriya baki daya ta rasa

Misis Dolapo Osinbajo, matar Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan jami’an sojin da suka mutu a hadarin jirgin sama a ranar Juma’a 21 ga Mayu, a Kaduna.

Babban hafsan sojan, Ibrahim Attahiru, tare da wasu hafsoshin sojan 10 sun rasa rayukansu a hadarin jirgi.

Wata sanarwa da Ofishin Mataimakin Shugaban ya aike wa Legit.ng ta nuna cewa Misis Dolapo, nan da nan da jin labarin hadarin, ya sanya ta kai ziyarta ga iyalan jami’an soja da suka mutu, tare da jajanta musu da danginsu, tare da taya su jimamin babban rashin.

KU KARANTA: Da Duminsa: Ba Za Mu Kara Farashin Man Fetur Yanzu Ba, Gwamnatin Buhari

Matar Osinbajo Ta Kai Ta'aziyya Gidan Marigayi Janar Attahiru, Ta Bayyana Kudurin Mijinta
Matar Osinbajo Ta Kai Ta'aziyya Gidan Marigayi Janar Attahiru, Ta Bayyana Kudurin Mijinta Hoto: Office of the Vice President
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Misis Dolapo a ranar Juma'a ta ziyarci matar marigayi COAS, tare da matar Shugaban Hafsun Tsaro, Misis Victoria Irabor.

A ranar Asabar, 22 ga watan Mayu, matar mataimakin shugaban kasan ta koma Fadar Ma’aikata, gidan COAS a Barikin Soja don zaman makoki tare da dangin marigayin da kuma kara jajantawa matar marigayi shugaban Sojojin.

A ranar Lahadi, 23 ga watan Mayu, Dolapo, tare da Misis Irabor, matan Shugaban Hafsun Sojin Ruwa, Hajiya Nana Aishat Gambo; da matar Shugaban Sojan Sama, Misis Elizabeth Olubunmi Amao, sun sake zuwa ganin matar marigayin don ta ya ta jaje.

Bayan haka, ta jagoranci wasu sun ziyarci matar marigayi Provost Marshal na sojojin Najeriya, Brig-Gen Olatunji Olayinka, da sauran matan manyan hafsoshin sojojin da suka kwanta-dama.

Misis Dolapo ta kuma kai ziyara zuwa sansanin NAF dake Abuja domin ganawa da mata da dangin duk sauran hafsoshin Sojan Sama da suka mutu a hadarin na Kaduna.

A can ta gana da iyalan jami'an da suka mutu, Flt Lt A Olufade, Sgt Adesina da ACM Oyedepo.

KU KARANTA: Watanni Bayan Caccakar Gwamnan Bauchi, Ortom Ya Yi Kira Ga Mutanensa Su Mallaki Bindiga

A wani labarin, Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a ranar Lahadi ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu tare da sauran sojoji 10 a ranar Juma'a yayin da Beechcraft 350 yayi hadari a filin sauka da tashin jiragen sama dake Kaduna.

Wadanda suka raka Aisha Buhari zuwa ta'aziyyar sun hada da ministan harkokin mata, shugaban mata ta jam'iyyar APC, shugaban cibiyar habaka mata da sauran mukarrabanta.

Ta nuna jimaminta tare da fatan rahama ga sojojin 11 da fatan Allah ya baiwa iyalansu hakurin jure rashinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel