Badakala: Majalisa Na Neman Akanta-Janar, Da Sauransu Kan Gibi a Kudaden da Aka Kwato
- Kwamitin wucin gadi kan binciken kadarorin da aka kwato ta nemi ganin Akanta-Janar na Tarayya
- Hakazalika kwamitin na majalisa ya nemi gwamnan CBN da shugaban EFCC, Abdurrasheed Bawa
- Kwamitin yana zargin ofishin Akanta-Janar na tarayya da ya zo ya yi bayanin wasu bangarorin kudi
Wani kwamitin majalisar wakilai ya nemi Akanta-Janar na tarayya kan gibin da ya lura dashi a kudaden da aka kwato daga babban bankin Najeriya.
Kwamitin, an kafa shi ne na wucin gadi a majalisar wakilai don binciken matsayin dukkan kadarorin da aka kwato na hukumomin tarayya tun daga shekarun 2002 zuwa 2020.
Shugaban kwamitin, Adejoro Adeogun, ne ya gabatar da bukatar neman a ranar Litinin lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin OAGF, Sabo Mohammed, a yayin bude zaman a Majalisar Dokoki ta Kasa, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Kada a Soke NYSC, a Horar da Matasa Kamar Sojoji Su Tunkari Matsalar Rashin Tsaro
Ya bayyana cewa, daga takardun da kwamitin ya samu, ya lura da yawan bambance-bambance da gibin da ke bukatar bayani daga Akanta-Janar na Tarayya.
Amma wakilin Akanta-Janar din ya nace cewa an mayar da kudaden da ake magana akansu ga babban bankin Najeriya (CBN).
“Ba ma cikin hukumar bincike. Duk abin da aka kwato kuma aka kawo mana, muna adanawa mu kula da su,” inji shi.
Kwamitin ya kuma nuna rashin jin dadinsa ga shugabannin hukumomin da suka tura wakilansu,.
A rahoton Premium Times, an ce kwamitin ya gayyaci Godwin Emefiele, Gwamnan CBN, Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya, Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, da sauransu.
KU KARANTA: An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa
A wani labarin, Majalisar Wakilai na duba yiwuwar dakatar da shirin bautar Kasa na NYSC, jaridar Punch ta ruwaito.
Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na Canji shekarar 2020, wanda ke neman soke dokar NYSC, an gabatar da shi a karatu na biyu.
Wanda ya dauki nauyin yunkurin, Mista Awaji-Inombek Abiante, a cikin bayanin shawarar, ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC.
Asali: Legit.ng