An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa

An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa

- 'Yan sanda sun cafke wasu bata-gari da suka yi awon gaba da tirela makare da fulawar Golden Penny

- Rahoto ya bayyana cewa, tuni aka kame su, kuma aka tura gaba don gudanar da bincike

- An ce sun daure direban ne tare da yaran motarsa kafin daga bisani suka yi awon gaba da tirelar

An kama wasu mutane hudu da ake zargi ‘yan fashi da makami ne da suka yi awon gaba da wata tirela mai dauke da fulawar Golden Penny kan babban titin Shagamu-Ijebu Ode na jihar Ogun.

Wadanda ake zargi da satar kayayyakin a ranar 16 ga Afrilu sun shiga hannun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun a ranar 5 ga Mayu, kamar yadda hukumomin 'yan sanda suka tabbatar wa gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, an ce wadanda ake zargin sun hada da Eze Anthony Sopruchuckwu, Eze Chijoke Edeh, Olalekan Ayodele Muritala da Samuel Johnson.

KU KARANTA: Majalisar Wakilai Na Duba Yiwuwar Soke Bautar Kasa ta NYSC Kwata-kwata a Najeriya

An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa
An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Oyeyemi ya ce an kamasu ne bayan wani “rahoto da aka gabatar a hedikwatar reshen Ikenne, cewa wata tirela, mai lamba ANG 57 LG, dauke da buhu 600 na Golden Penny wanda Ahmed Tiamiyu ke tukawa an sace ta a kan babbar hanyar.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa an dauki direban tirelar da yaron motarsa ​​zuwa daji, inda aka daure hannayensu a bayansu sannan aka dinke bakinsu, kafin a dauke babbar motar da kuma fulawar.

Bayan rahoton, Kwamishinan 'yan sanda a Ogun, Edward Ajogun, ya ce ya ba da umarnin a tura batun zuwa Ofishin Bincike na Musamman a hedikwatar 'yan sanda na jihar, Eleweran, Abeokuta, don gudanar da bincike cikin hikima, Prime Times News ta ruwaito.

KU KARANTA: Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen gurfanar da mutane 5,800 da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne.

Chioma Onuegbu, Shugabar hadaddiyar kungiyar masu shigar da kara kuma Mataimakiyar Daraktan gabatar da kararraki a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, ita ce ta bayyana hakan a Abuja a karshen makon da ya gabata yayin ganawa da manema labarai da Gidauniyar Wayamo.

Onuegbu ta ce ma’aikatar ta tantance takardun kara 800 daga cikin mutum 1,000 da ake zargi wadanda aka gabatar da shaidu a shekarar 2019, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel