Mutum Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Gas a Bauchi

Mutum Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Gas a Bauchi

- Fashewar tukunyar gas a garejin makanikai a garin Azare ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a jihar Bauchi

- Mai tirelan ya shiga garejin da nufin a yi masa gyara ne kwatsam sai tukunyar gas din ta fashe ta kama da wuta a lokacin da ake gyara

- Direba ya rasu yayin da ya ke kokarin fitar da tirelan daga garejin kana wutar ta yi wa kimanin mutum 11 rauni suna asibiti ana musu magani

Mutane biyu sun mutu, kimanin wasu mutanen 11 sun samu raunuka yayin da tukunyar gas ta fashe a wani gareji a garin Azare da ke karamar hukumar Katagum na jihar Bauchi, The Punch ta ruwaito.

An ruwaito cewa hadarin ya faru ne a cikin wani gareji da ke kan layin Jama'ar da rana a ranar Litinin.

Mutum Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Gas a Bauchi
Mutum Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Gas a Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP

Wata majiya daga Azare da aka yi hira da shi ta wayar tarho ya ce direban wani trela ne ya shiga garejin da nufin a yi masa gyara a shagon mai walda.

"A lokacin da ake gyaran ne tukunyar gas da wani mai waldan ke amfani da ita ta fashe nan take.

"Wutar da ta taso daga fashewar tukunyar gas din ta bazu a garejin inda nan take wurare da dama suka kama da wuta ta kuma yi wa mutane rauni.

"Wannan ya haifar da tashin hankali a yayin da mutane ke ta kokarin tserewa daga wutar, garin hakan wasu da dama cikinsu suka kone," in ji shi.

A cewar majiyar, direban ya mutu a yayin da ya ke kokarin fitar da tirelan daga garejin.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

A lokacin hada wannan rahoton, mutane 11 ne aka ce sun jikkata sakamakon mugun kuna kuma ana musu magani a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da Babban Asibitin Azare.

An yi kokarin ji ta mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil amma hakan ya ci tura.

A wani labarin, Wasu mazauna garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa na jihar Niger, a ranar Litinin sun tare titin Abuja-Kaduna suna zanga-zanga kan yawan sace mutane da ake yi a garin,The Cable ta ruwaito.

Garin na Gauraka na kan babban hanyar Abuja zuwa Kaduna ne.

Masu zanga-zangar sun dakatar da zirga-zirgan motocci a kan titin yayin da suke kona tayoyi domin janyo hankulan mutane.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel