Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

- Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi magana da matar marigayi COAS Attahiru a waya tare da matan sauran jami'an da suka rasa ransu

- Buhari ya bayyana marigayi Ibrahim Attahiru da gwarzon soja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen aiki ga ƙasar sa Najeriya

- Shugaban ya kuma roƙi matan da su yayyafa wa zuciyoyinsu ruwan sanyi, yana mai cewa Najeriya ba zata taɓa mantawa da sadaukarwar mazajen su ba

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi wa Hajiya Fati ta'aziyya, matar marigayi shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahim Attahiru, ta wayar salula.

KARANTA ANAN: Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Janar Attahiru tare da wasu manyan jami'an soji sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgi da ya rutsa dasu a jihar Kaduna.

Anyi jana'izarsu sannan aka burne su a maƙabartar rundunar soji dake babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai taimaka wa shugaban wajen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita @BashirAhmad.

Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya
Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya Hoto @BashirAhmad
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon soja wanda yayi yaƙi ba ɗare ba rana ga ƙasar sa Najeriya har ƙarshen rayuwarsa.

Jawabin Bashir Ahmad, yace:

"Da yammacin nan, shugaba Buhari yayi magana da Mrs. Fati Ibrahim Attahiru, matar marigayi shugaban rundunar sojin ƙasa da kuma sauran iyalan jami'an sojin da suka rasa ransu."

"Buhari ya bayyana marigayi COAS Attahiru a matsayin jarumi, gwarzo wanda yayi yaƙi domin Najeriya har zuwa ƙarshen rayuwarsa. Shugaban ya kuma yaba da irin sadaukarwar da jami'am sojin suka yi, waɗan da suka rasa rayuwarsu da kuma jami'an tsaro baki ɗaya."

KARANATA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Yan Bindiga, Sun Kuɓutar da Mutanen da Suka Sace a Jihar Kaduna

"Ya ƙara da cewa yan Najeriya zasu cigaba da yaba musu da basu dukkan goyon baya ba tare da tsoro ba, hakan zai ƙara ƙarfafa wa sojojin mu guiwa wajen fuskantar barazanar tsaro da ƙasar mu ke fama da ita."

"Ya tabbatar wa da matan cewa Najeriya ba zata taɓa mantawa da wannan ƙololuwar sadaukarwar da mazajen su suka yi ba. Ya roƙe su da su zuba wa zuciyoyin su ruwan sanyi su ɗauki dangana a wannan yanayi mai matuƙar wahala a garesu."

Shugaba Buhari ya umarci ma'aikatar tsaro da hedkwatar tsaro ta ƙasa da su samar da duk wani abu da ya dace ga iyalan mamatan domin rage musu radaɗin wannan babban rashi da suka yi.

A wani labarin Kuma Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano

Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewa aƙalla mutum 64 ne suka jikkata lokacin da wata tankar mai ta fashe a Sharaɗa.

An gano cewa da yawa daga cikin waɗanda abun ya shafa sun zo kallon yadda motar ta faɗi ne kafin daga baya ta fashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel