Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

- Allah ya yi wa tsohon ministan zamanin Sardauna rasuwa bayan shafe shekaru 97 a duniya

- Wata sanarwa ta bayyana cewa, ministan ya ga zuri'a da dama kafin ya riga mu gidan gaskiya

- Hakazalika an bayyana manyan 'ya'yansa da kuma adadin surukansa, ciki har da minisatan Buhari

Allah ya yiwa Alhaji Abdullahi Danburan Jada rasuwa da sanyin safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Mayu, 2020. Ya rasu yana da shekaru 97 a duniya.

Jada ya kasance tsohon ministan kiwon lafiyar dabbobi, gandun daji da Arewacin Kamaru a zamanin tsohon Firimiya na Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.

Wata sanarwa da aka aike wa Legit.ng Hausa ta ce, "marigayin wanda aka haifa a Nasarawa Jada a shekarar 1924, a yankin Arewacin Kamaru na lokacin, ya yi makarantar firamare ta Yola da Yola Middle School a shekarun 1937 da 1944.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari Ta Shirya Gurfanar da Wadanda Ake Zargin ’Yan Boko Haram Ne 5,800

Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

"Alhaji Danbuaran ya yi karatu a Makarantar Noma ta Samaru, inda ya yi karatu tsakanin 1948 zuwa 1952. Sannan ya zama mai kula da aikin gona a Adamawa har zuwa 1955, lokacin da aka nada shi hakimi daga baya kuma aka zabe shi.

Sanarwar ta bayyana cewa, Alhaji Jada ya ga 'ya'ya, jikoki, tattaba-kunne da sauransu zuri'a dama kafin rasuwarsa.

Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: UGC

"Daga cikin yaransa akwai: Usman Danburam, Ibrahim Danburan, Dr Nafisa Mohammed, tsohuwar shugabar hukumar Ilimin yaki da jahilci.

Surukansa kuwa sun hada da: "Dr Mahmud Tukur, Dr Dahiru Mohammed, Dr Bashir Gwandu, Ministan Aikin Gona na yanzu Sabo Nanono, da Alhaji Bakari."

KU KARANTA: Matar Osinbajo Ta Kai Ta'aziyya Gidan Marigayi Janar Attahiru, Da Sauran Jami'ai

A wani labarin, Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe mutane uku a kauyen Garin Zogo da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

Sun kuma fatattaki kauyuka takwas a karamar hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake tabbatar da hare-haren, Kansilan da ke wakiltar yankunan, Ibrahim Muhammad Saraki ya ce an kaiwa Garin Zogo hari ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10:30 na dare.

“Sun kashe mutane uku sannan suka ji wa daya rauni. Sun kuma yi awon gaba da dabbobi, sun kutsa cikin shaguna da yawa sun kwashe kayan da ba a san adadinsu ba,” inji shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel