Gwamnatin Buhari Ta Shirya Gurfanar da Wadanda Ake Zargin ’Yan Boko Haram Ne 5,800

Gwamnatin Buhari Ta Shirya Gurfanar da Wadanda Ake Zargin ’Yan Boko Haram Ne 5,800

- Gwamnatin tarayya za ta gurfanar da wadanda ake zargi 'yan Boko Haram ne kimanin 5,800

- Gwamnati ta ce za hare-hare da kuma annobar Korona ne ta hana gurfanar dasu a 2019 da 2020

- Gwamnatin Najeriya na ci gaba da aiki don tabbatar da gurfanar da masu laifi da masu daukar nauyinsu

Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen gurfanar da mutane 5,800 da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne.

Chioma Onuegbu, Shugabar hadaddiyar kungiyar masu shigar da kara kuma Mataimakiyar Daraktan gabatar da kararraki a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, ita ce ta bayyana hakan a Abuja a karshen makon da ya gabata yayin ganawa da manema labarai da Gidauniyar Wayamo.

Onuegbu ta ce ma’aikatar ta tantance takardun kara 800 daga cikin mutum 1,000 da ake zargi wadanda aka gabatar da shaidu a shekarar 2019, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Watanni Bayan Caccakar Gwamnan Bauchi, Ortom Ya Yi Kira Ga Mutanensa Su Mallaki Bindiga

Gwamnatin Tarayya ta shirya gurfanar da wadanda ake zargi da Boko Haram 5,800
Gwamnatin Tarayya ta shirya gurfanar da wadanda ake zargi da Boko Haram 5,800 Hoto: ocdn.eu
Asali: UGC

Ta ce munanan hare-haren da aka kai a yankin arewa maso gabas da kuma annobar Korona sun shafi fara shari'ar a shekarar 2019 da 2020.

Ta ce kwanan nan sojoji suka sake tura wasu sabbin fayal na kararraki 5,000 daga Maiduguri, jihar Borno, wanda yanzu haka ma’aikatar ke aiki tukuru don aiwatar da su.

Onuegbu ta ce daga cikin kararraki guda 1,000, an yi shawarin a saki wadanda ake zargi 170 saboda rashin kwararan hujjoji don gurfanar da su.

Ta ce a baya ma`aikatar ta kammala irin wannan shari’ar a watan Oktoba na 2017, Fabrairu 2018 da Yuni 2018 kuma ana shirin shiga mataki na hudu na gurfanarwar.

Gwamnatin tarayya na ci gaba da aiki don tabbatar da kame masu aikata laifuka da masu daukar nauyin aikata laifuka a fadin kasar tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana a baya cewa za ta gurfanar da kimanin wadanda ake zargi da daukar nauyin kungiyar Boko Haram da masu canjin kudi da aka kama a wani samame da aka gudanar a kasar a watan Afrilu, The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Da Duminsa: Ba Za Mu Kara Farashin Man Fetur Yanzu Ba, Gwamnatin Buhari

A wani labarin, Kwamitin Jagorancin Shugaban Kasa (PSC) kan cutar Korona ya fitar da sunayen matafiya 90 da ya ayyana a matsayin ‘Mutanen da ake nema, saboda gujewa kebewar kwanaki bakwai, PM News ta ruwaito.

Kebewa ya zama tilas ga mutanen da suka zo daga kasashe masu tsanani, kamar su Brazil, Indiya da Turkiya, inda ake da yawaitar cutar Korona.

Shugaban kwamitin kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce wadanda suka yi kuskuren sun hada da ’yan Najeriya 63 da 'yan kasashen waje 27.

Asali: Legit.ng

Online view pixel