Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe

Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe

- Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da yin artabu da yan bindiga a ƙauyen Magami dake jihar Zamfara Ranar Asabar

- Kakakin hukumar yan sandan yace an kashe musu jami'ai biyu sakamakon lamarin, yayin da yan bindiga da yawan gaske suka baƙunci lahira

- Kwamishinan yan sandan jihar ya gargaɗi yan bindigan dake jihar su aje makamansu a zauna lafiya ko kuma su cigaba da ganin fushin hukuma

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kashe yan bindiga da dama ranar Asabar da daddare yayin da suka yi ƙoƙarin kai hari ƙauyen Magami, ƙaramar hukumar Gusau, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru ta Wayar Salula

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin yan sandan jihar, Shehu Muhammed, ya fitar a Gusau.

Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe
Hukumar Yan Sanda Ta Tabbatar da Fafatawa da Yan Bindiga, Ta Bayyana Jami’ai, Yan Bindigan da Aka Kashe Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace: "Ranar Asabar da daddare, mun samu rahoton cewa yan bindiga sun shiga garin Magami da niyyar kaiwa al'ummar garin hari."

"Nan take kwamishinan yan sanda, CP Hussaini Rabiu, ya umarci jami'an yan sanda da suka haɗa da jami'an Operation Puff Adder da sukai ɗauki domin tabbatar da kare mutane da dukiyoyin su."

"Jami'an sun kai ɗauki inda suka yi musayar wuta da maharan, a sakamakon haka an sami nasarar daƙile harin, yayin da adadi mai yawa na yan bindigan suka mutu, sauran kuma suka gudu da raunin harbi a jikinsu."

"Biyu daga cikin jami'an mu sun rasa rayuwarsu a yayin da suke ƙoƙarin kare al'umma, amma babu wani farar hula da ya mutu a harin." Inji shi.

KARANTA ANAN: AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa kwamishinan ya ƙara tura wasu jami'ai na musamman domin su cigaba da duba dajin dake yankin da nufin kare sauran ƙauyuka daga harin yan ta'adda.

Yace: "CP ya kira yi yan bindigan dake jihar ko dai su aje makaman su a zauna lafiya ko kuma su cigaba da fuskantar fushin hukuma."

"Ya kuma roƙi jami'an yan sanda da su kare kansu kuma su kare mutanen dake yankin su daga dukkan wasu hare-haren yan bindiga."

Rahoton da Leardership ta ruwaito ya nuna cewa yan bindiga sun kai hari caji ofis ɗin yan sanda a ƙauyen Magami, inda suka kashe jami'ai biyu tare da yin awon gaba da bindigu AK-47 guda biyu.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Fatattaki Yan Bindiga, Sun Kuɓutar da Mutanen da Suka Sace a Jihar Kaduna

Sojoji sun sami nasarar ƙuɓutar da wasu mutane da yan bindiga suka yi niyyar sace wa a ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kuɓutar da mutanen, yace mafi yawancin su matan aure ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262