Da Duminsa: Ba Za Mu Kara Farashin Man Fetur Yanzu Ba, Gwamnatin Buhari
- Gwamnatin tarayya ta yi martani kan shawarin gwamnonin Najeriya na karin farashin man fetur
- Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi ittifakin cewa ya kamata a kara farashin man fetur zuwa sama da 300
- Gwamnati ta gargadi masu ruwa da tsaki a jigilar man na fetur cewa su guji tsoma kasar cikin wani yanayi
Gwamnatin Tarayya ta ce ba zata kara farashin famfo na man fetur cikin gaggawa ba, a cewar Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Daily Trust ta ruwaito.
Sylva ya fadi haka ne yayin da yake martani kan shawarar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) cewa farashin mai ya kamata ya kasance tsakanin N380 da N408.5 kowace lita.
Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a ranar Laraba 20 ga watan Mayu ta shawarci gwamnatin tarayya cewa ta kara farashin famfo na man fetur tare da cire tallafinsa ba tare da bata lokaci ba, Arise Tv ta ruwaito.
KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Kame 'Yan Bindiga 4, Sun Ceto Wadanda Aka Sace 2
Shawarwarin da gwamnonin suka bayar ya haifar da fushi da fusata a duk fadin kasar kamar yadda yawancin 'yan Najeriya suka ce hakan zai ninka wahalhalu ga 'yan kasar.
Amma a nasa martanin, Sylva ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa ba za a kara farashin man a watan Yuni ba.
"Ya zama dole a tabbatar wa 'yan Najeriya cewa duk da dimbin nauyin da ke kan farfadowa, Gwamnatin Tarayya ba za ta kara farashin man fetur cikin gaggawa ba don yin la’akari da gaskiyar kasuwar yanzu.”
“Za a bar farashin mai kamar yadda yake ya ci gaba a cikin watan Yuni har sai an kammala hada-hadar kungiyar kwadago.
"Wannan bayani ya zama dole bisa la'akari da rahotanni na baya-bayan nan dangane da kudurin kungiyar Gwamnonin Najeriya na kara farashin famfo na man fetur.
Hakazalika ya yi kira ga masu hada-hadar man fetur da su guji tsoma kansu cikin wasu abubuwan da ka iya kawo cikas ga rarraba man fetur a fadin kasar.
KU KARANTA: Rahoto: Akalla jami'ai 127 Aka Kashe a Yankunan Kuduncin Najeriya, An Kona Ofisoshi 25
A wani labarin, Kamfanin rarraba wutar lantarki a jihar Kaduna, Kaduna Electric ya sake bai wa abokan huldarsa hakuri game da rashin wuta a jihar tsawon kwana hudu sakamakon yajin aikin kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC).
A makon nan jihar Kaduna ta rikice da zanga-zanga biyo bayan korar wasu ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi, lamarin da ya tunzura dubban jama'a.
Kungiyar kwadago ta Najerita (NLC) ta tsundumawa yajin aiki sakamakon korar abokan aikinsu, lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon.
Asali: Legit.ng