Watanni Bayan Caccakar Gwamnan Bauchi, Ortom Ya Yi Kira Ga Mutanensa Su Mallaki Bindiga
- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortum ya bukaci 'yan jiharsa da su mallaki bindigogi da makamai
- A cewarsa, wannan wani yunkuri ne na kokarin kare kansu daga Fulani makiyaya a fadin jihar ta Benue
- Sai dai, gwamnan a baya ya caccaki gwamnan jihar Bauchi bisa irin wannan kira na daukar makami daga makiyaya
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom a jiya Lahadi 24 ga watan Mayu, ya bukaci mutanen jiharsa da su samo lasisin bindiga daga kananan hukumomi domin kare kansu, The Nation ta ruwaito.
Ya yi wannan magana ne a cocin mabiya addinai da yammacin jiya Lahadi a Chapel of Grace na gidan gwamnati dake Makurdi don kammala shirin kwanaki bakwai na addu’o’i da azumi don zaman lafiya a jihar.
“Ba zan kara sanar da mutuwar wadanda Fulani makiyaya suka kashe ba, ku tashi ku kare kanku da makaman da doka ba ta hana ba, kwari da baka, mashi da wukake. Ku samo lasisin bindigogi daga karamar hukuma ku yi amfani da su don kare kanku,” inji shi.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 3, Sun Fatattaki Kauyuka 8 a Sakkwato
Ya kara da cewa muddin ya kasance cikin kiyaye dokokin ubangiji, babu wani makami da aka kera shi da zai yi tasiri akansa.
"Ubangiji ya tabbatar min a wani lokaci can cewa, duk lokacin da nake rayuwa da kiyayeshi, babu wani makami da aka kera da zai yi tasiri akaina" in ji shi.
Sai dai, a baya gwamnan ya caccaki gwamnan jihar Bauchi bisa kira ga Fulani makiyaya kan cewa su mallaki bindigogi don kare kansu.
A ranar Litinin, 22 ga watan Fabrairu, gwamna Ortom ya zargi takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, da kasancewa dan ta’adda bisa lafazin da yayi na goyon bayan makiyaya su dauki bindiga don kare kansu, Channels Tv ta ruwaito.
Gwamna Ortom wanda ya yi wannan zargin lokacin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Benue ya ce Gwamna Mohammed ya kasance dan ta’adda saboda goyon bayan haramtattun makamai da makiyayan kasashen waje ke yi.
KU KARANTA: Musulman Duniya Sun Yabawa Saudiyya Bisa Hannu a Dakatar da Rikici a Zirin Gaza
A wani labarin, Yayin da ake jana'izar Janar Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsan soji, da wasu 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Abuja, gwamnoni da yawa sun hallara zuwa Kano don halartar bikin dan Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a.
Wannan ya haifar da cece-kuce daban-daban daga 'yan Najeriya wadanda ke ganin manyan hafsoshin sojojin da suka mutu a bakin aiki ba su sami irin girmamawar da ta dace da su ba.
Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ba su halarci jana'izar ba wacce ta samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.
Asali: Legit.ng