Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru sun bayyana

Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru sun bayyana

- Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasan Najeriya ta ziyarci matar marigayi Laftanala Janar Ibrahim Attahiru

- Ta samu rakiyar ministan harkokin mata, shugaban mata ta jam'iyyar APC da sauran mukarrabanta

- Aisha Buhari ta nuna jimaminta tare da yin addu'ar gafara da kuma fatan iyalan mamatan zasu samu hakurin jure rashin

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a ranar Lahadi ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu tare da sauran sojoji 10 a ranar Juma'a yayin da Beechcraft 350 yayi hatsari a filin sauka da tashin jiragen sama dake Kaduna.

Wadanda suka raka Aisha Buhari zuwa ta'aziyyar sun hada da ministan harkokin mata, shugaban mata ta jam'iyyar APC, shugaban cibiyar habaka mata da sauran mukarrabanta.

Ta nuna jimaminta tare da fatan rahama ga sojojin 11 da fatan Allah ya baiwa iyalansu hakurin jure rashinsu.

KU KARANTA: Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya

Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru suna bayyana
Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru suna bayyana. Hoto daga @aishambuhari
Asali: Twitter

Kamar yadda Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram, "Na kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru.

"Na samu rakiyar ministan harkokin mata, wakiliyar mata ta APC, shugaban cibiyar cigaban harkokin mata da sauran mukarrabai.

"Mutuwar Attahiru da sauran sojojin dake kan jirgin nan babban rashi ne ga iyalansu da kuma kasa baki daya.

"Allah ya gafarta musu kuma ya baiwa iyalansu hakurin jure wannan rashin da ba za a iya maye masu gurbin shi ba."

KU KARANTA: Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauke tutoci domin karrama marigayi Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasa da sauran sojoji 10 da suka rasa rayukansu yayin hatsarin jirgin sama na Kaduna.

Sojojin 11 suna cikin jirgin saman sojin Najeriya yayin da yayi hatsari kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na farar hula dake Kaduna a ranar Juma'a.

An shirya cewa Attahiru zai halarci taron yaye kananan sojoji a Kaduna a ranar Asabar.

Kamar yadda takardar da aka fitar a ranar Lahadi daga Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, ta bayyana, an bukaci sauke tutoci a dukkan gine-ginen gwamnati da gidajenta na tsawon kwanaki uku.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel