Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Jihar Ogun, Sun Sace Ɗalibi, Lakcara da Wasu Mutum Biyu

Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Jihar Ogun, Sun Sace Ɗalibi, Lakcara da Wasu Mutum Biyu

- Yan bindiga sun sace mutum huɗu a wasu hare-hare da duka kai jihar Ogun, cikin su harda wani ɗalibin jami'ar FUNAAB

- Hukumar jami'ar FUNAAB ta tabbatar da sace ɗalibinta, tace takai rahoto hedkwatar yan sanda

- Kakakin rundunar yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da kai hare-haren a jihar Ogun

Yan Bindiga sun sace mutum huɗu, cikin su harda wani ɗalibi a wasu hare-hare da suka kai jihar Ogun tsakanin Laraba Zuwa Asabar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano

Yan bindigan sun kai hari na farko ne a Ijebu–Ode ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da wata Lakcara kuma mataimakiyar darakta, Mrs B. L. Abimbola, a jami'ar ilimi Tai Solarin (TASUED).

Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Jihar Ogun, Sun Sace Ɗalibi, Lakcara da Wasu Mutum Biyu
Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Jihar Ogun, Sun Sace Ɗalibi, Lakcara da Wasu Mutum Biyu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An kuma sake kai hari a wata gona dake ƙauyen Abule Itoko ƙaramar hukumar Odeda jihar Ogun, inda aka sace wani ɗalibi dake shekarar karatu ta huɗu a jami'ar koyon aikin gona (FUNAAB), Abekuta tare da wasu mutane biyu.

An gano cewa ɗalibin FUNAAB da aka sace ya kasance yana aiki a wannan gonar na tsawon shekaru uku domin samun kuɗin da zai biya kuɗin karatunsa,.kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hukumar jami'ar FUNAAB ta bayyana dalibin da aka sace da suna, Toyinbo Nathaniel Olayinka.

KARANTA ANAN: Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Daraktan yaɗa labarai na jami'ar FUNAAB, a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi, yace an sace ɗalibin ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Ranar Asabar.

Yace: "Wasu yan bindiga sun sace ɗalibin jami'ar mu, Toyinbo Nathaniel Olayinka, a wata gona dake Abule-Itoko, ƙaramar hukumar Odeda."

"Hukumar makaranta ta kai rahoton sace ɗalibin ga hedkwatar hukumar yan sanda ta jihar Ogun, kuma muna cigaba da ƙoƙari domin ganin an sako ɗalibin cikin ƙoshin lafiya."

Kakakin hukumar yan sanda, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sace Abimbola ta TASUED, amma har yanzun yaƙi maida martani kan tambayar da aka masa game da sace ɗalibin FUNAAB ba.

A wani labarin kuma Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah

Rahotanni daga ƙasar Saudiyya na nuni da cewa wani mutumi yayi yunƙurin kashe limamin ka'aba ranar Jumu'a.

Hukumar dake kula da masallatai biyu masu daraja a ƙasar ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel