Da Muninsa: Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

Da Muninsa: Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

- Wani ɗan majalisar tarayya a jihar Cross Rivers ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma Jam'iyya mai mulki ta APC

- Mike Etaba, daga jihar Cross Rivers yace yana tare da gwamnan jihar, Ben Ayade, duk inda ya koma

- Ana ganin har yanzun akwai sauran yan majalisar da ka iya sauya sheƙa a jihar cikin kwanaki kaɗan masu zuwa

Wani ɗan majalisar tarayya, Mike Etaba, ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Aƙalla Mutum 64 Sun Jikkata Yayin Da Tankar Man Fetur ta Fashe a Kano

Etaba, wanda ya fito daga jihar Cross Rivers, yace ya yanke wannan hukunci ne sabida Gwamnan jihar, Ben Ayade, ya koma APC.

Wannan na zuwa ne biyo bayan ficewar gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, daga PDP zuwa APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yayi rijista da APC a mazaɓarsa ta Apiapum, ƙaramar hukumar Obubra jihar Cross Rivers.

Da Muninsa: Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC
Da Muninsa: Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mike Etaba na wakiltar mazaɓar Obubra/Etung a majalisar dokoki ta ƙasa.

Ɗan majalisar ya bayyana kanshi a matsayin mabiyin gwamna Ayade a kowane yanayi, kuma zai cigaba da kasancewa tare da gwamnan har bayan 2023.

KARANTA ANAN: Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro

Etaba yace matakin da gwamnan ya ɗauka na canza sheƙa zuwa APC shine ya dace a wannan lokacin domin kawo wa al'ummar Cross Rivers cigaba.

Ana raɗe-raɗin cewa aƙalla wani ɗan majalisa ɗaya ka iya sauya sheka zuwa APC a jihar cikin kwanaki kaɗan masu zuwa.

A wani labarin kuma Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Ofishin gwamnatin Amurka a Najeriya ya jajantawa yan Najeriya a kan rasuwar shugaban soji tare da wasu sojoji 10 a haɗarin jirgi.

Catriona Laing, kwamishinan Burtaniya a Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan faruwar hatsarin jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel