Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru
- Ofishin gwamnatin Amurka a Najeriya ya jajantawa yan Najeriya a kan rasuwar shugaban soji tare da wasu sojoji 10 a haɗarin jirgi
- Catriona Laing, kwamishinan Burtaniya a Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan faruwar hatsarin jirgin
- Shugaba Rundunar soji, Ibrahim Attahiru, tare da wasu mutum 10 sun rasa rayuwarsu a hatsarin jirgi ranar Jumu'a 21 ga Mayu
Ofishin gwamnatin Amurka a Najeriya ya taya ƙasar jimamin mutuwar shugaban sojin ta, Lt. Gen Ibrahim Attahiru, inda yace wannan babban rashi ne.
KARANTA ANAN: IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu
Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da ofishin yayi a shafinsa na twitter ranar jumu'a da daddare wanda Legit.ng ta gani.
Rubutun yace:
"A dai-dai wannan lokaci mai matuƙar wahala Najeriya, lokacin da ake matuƙar buƙatar tsaro da zaman lafiya, muna miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga yan uwan janar Attahiru da kuma yan uwan waɗanda hatsarin jirgin ya ritsa da su."
Hakanan kuma, kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta bayyana damuwarta kan mutuwar COAS.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga
A shafin ta na kafar sada zumunta twitter, Laig tace:
"Nayi matuƙar kaɗuwa da takaicin jin wannan labarin mara daɗi, muna miƙa ta'aziyyar mu ga makusantan marigayi Janar Attahiru da dukkan makusantan sauran jami'an da suka rasa rayuwarsu. Mun tura ta'aziyyar mu ga shugaban ƙasa Buhari da rundunar Soji."
Shugaban rundunar soji, Ibrahim Attahiru, tare da wasu jami'ai 10 sun rasa rayuwarsu a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa dasu a Kaduna.
Rundunar soji tayi bayanin cewa COAS na kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna ranar Jumu'a 21 ga watan Mayu yayin da mummunan lamarin ya faru dashi.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yace yayi matuwar kaɗuwa da hatsarin jirgin wanda yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojin sa da wasu jami'ai 10.
A wani.labarin kuma Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah
Rahotanni daga ƙasar Saudiyya na nuni da cewa wani mutumi yayi yunƙurin kashe limamin ka'aba ranar Jumu'a.
Hukumar dake kula da masallatai biyu masu daraja a ƙasar ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sada zumunta.
Asali: Legit.ng