'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Uba da Dansa a Babban Birnin Tarayya Abuja

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Uba da Dansa a Babban Birnin Tarayya Abuja

- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani uba da dansa a wani yankin babban birnin tarayya, Abuja

- Rahoto ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun zo su sama da 20 suka yi barna na sama da awa daya

- Yankunan babban birnin tarayya Abuja na ci gaba da fuskantar sace-sacen mutane da harin 'yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Lahadi sun mamaye yankin Kuchiko a karamar hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) inda suka yi awon gaba da wani mazauni da dansa.

Daily Trust ta tattaro cewa ’yan bindigan wadanda yawansu ya kai ashirin sun afka wa yankin, wanda aka fi sani da El-Rufa’i Estate, da karfe 12 na dare kuma suka fara harbi ba kakkautawa.

Bayan sun fi karfin jami’an tsaro, ‘yan bindigan, sun yi amfani da wukake da adduna, suka nufi gidan wanda aka sacen suka yi garkuwa da shi da dan nasa.

KU KARANTA: Shekau Gwarzo Ne: Dan Majalisa Ya Kori Mai Taimaka Masa Saboda Yabon Shekau

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Uba da Dansa a Babban Birnin Tarayya Abuja
'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Uba da Dansa a Babban Birnin Tarayya Abuja Hoto: spread.ng
Asali: UGC

An tattaro cewa maharan, wadanda suka yi barna na tsawon awa daya, daga baya sun wuce zuwa gidan wani mazauni kuma suka yi yunkurin sace shi.

Ko da yake, isowar sojoji daga Kwalejin Tsaro ta Bwari a kan lokaci, ya taimaka a halin da ake ciki bayan sun yi musayar wuta da 'yan bindigan.

Wasu mazauna yankin, wadanda suka ba da labarin abin da ya faru da su, sun yi kira ga hukumomi da su karfafa tsaro a kewayen yankin.

Jami'in 'yan sanda na Shiyya a Yankin Bwari (DPO) bai samu damar tabbatar da labarin ba kamar yadda yake a lokacin hada wannan rahoto.

Lamarin sace-sacen mutane na kara yawa a yankunan arewain Najeriya, wanda ya tsoma wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja cikin mazan fargaba.

KU KARANTA: Yadda ISWAP Ta Yi Amfani da Mata da Yara Wajen Hallaka Shekau

A wani labarin, Mista Gabriel Ubah, jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a Filato, ya ce rundunar ta kama masu garkuwa da mutane hudu kuma ta kubutar da mutane biyu daga hannun su, The Guardian ta ruwaito.

A wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho a ranar Alhamis a karamar hukumar Mangu da ke jihar, Ubah ya ce rundunar tana kuma kokarin ceto sauran mutanen biyu da aka sace daga hannun masu garkuwar.

Ya tuna cewa masu garkuwar sun aikatata'addanci a Gaya Layout kusa da Chichim Quarters a garin Mangu da misalin karfe 8.30 na dare a ranar 19 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel