Yadda ISWAP Ta Yi Amfani da Mata da Yara Wajen Hallaka Shekau
- Rahoto ya bayyana kungiyar ISWAP ta tura mata da kananan yara wajen yakar Boko Haram
- An ce an tura yara masu kananan shekaru ne suka afkawa shugaban kungiyar Boko Haram
- Duk da cewa rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da mutuwar Shekau ba, akwai alamun ya mutu
Mata da yara masu kananan shekaru na daga cikin mayakan da suka yi artabu da Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, a daya daga cikin fadace-fadace mafi muni da yayi a rayuwarsa.
Wasu majiyoyi game da harin sun shaida wa Daily Trust cewa ISWAP ta yi amfani da mayaka 'yan tsakanin shekara 12 zuwa 30 a harin.
An ce duka bangarorin sun yi asara a artabun amma sansanin na Shekau ya fi yin asara yayin da shugaban ya yi kunar bakin wake ya kashe kansa ko kuma ya samu munanan raunuka da suka sa da wuya ya rayu.
Sai dai, Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu ba ta samu labarin mutuwar shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau ba, Reuben Abati ya ruwaito.
KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Kame 'Yan Bindiga 4, Sun Ceto Wadanda Aka Sace 2
An ce an horar da mayakan na ISWAP a Libya, Somalia da sauran kasashen waje.
An ce sun shirya sosai don auka wa shugaban na Boko Haram da ya share shekaru yana addabar al'ummar arewa maso gabashin Najeriya.
"Su (mayakan) hakika 'ya'yan wasu 'yan kungiyar ISWAP ne da aka kashe a wani lokaci," in ji daya daga cikin majiyoyin.
“Wasu kuma matasa ne da aka samo su a yayin samame a tsibirai da yawa da ke kewayen Tafkin Chadi.
"Kungiyar ISWAP ta zabi matasan cikin ruwan hankali. Don haka ya kasance mafi sauki a daukarsu yayin da wasu daga cikin matasan suka yarda suka shiga kungiyar wasu kuma da karfi aka tilasta su.
“Wasu daga cikinsu an haife su ne a lokacin yakin wasu kuma kanana ne lokacin da iyayen su suka shiga kungiyar a wajajen 2002. Bayan iyayensu sun mutu saboda rashin lafiya ko kuma arangama da sojojin Najeriya, yaran sun shiga tafiyar.
"Lokacin da kungiyar ta rabu biyu a 2016 , wadanda suka kaura da kansu ko kuma aka tilasta masu da karfi zuwa gabar tafkin Chadi a karkashin inuwar ISWAP sun goge a fagen horo saboda an dauke su zuwa Libya don samun horo kan yakar kungiyoyin asiri da sauran dabaru.
“An tura wasu zuwa kasashen Syria da Somalia… An kai su kasashen waje da yawa don samun horo. Saboda haka, wadanda suka dawo musamman tsakanin Maris zuwa Afrilu na wannan shekara sun taka rawa wajen tunkarar Shekau a cikin kwanakin da suka gabata.
"Sun kaddamar da mummunan farmaki tare da sauran manyan kwamandoji da mayakan da ke kasa kuma sun yi nasarar karbe iko.
Wata majiyar kuma ta ce an horar da wasu daga cikin matasa 300 din a matsayin "Likitocin kiwon lafiya, da masu ba da agajin gaggawa, da injiniyoyi, da kwararru a fannin IT, da kwararrun kan bam da kuma kanikanci."
Ya kara da cewa daga cikinsu akwai mata "wadanda ke aikin jinya da masu dafa abinci yayin da wasu kuma ke da kwarewar sarrafa bindiga, ma'ana za su iya shiga cikin yaki."
KU KARANTA: Da Duminsa: Ba Za Mu Kara Farashin Man Fetur Yanzu Ba, Gwamnatin Buhari
A wani labarin, Ƙasar Amurka ta bayyana cewa ƙungiyar ISWAP ba zata samu ko sisi ba daga cikin dala miliyan $7m data sa kan duk wanda ya gano inda Abubakar sheƙau yake.
Yayin da take martani kan rahoton mutuwan shugaban mayaƙan Boko Haram ɗin, Amurka tace ba zata baiwa ƙungiyar dake ƙarƙashin ISIS ba.
Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da sashin shari'a na ƙasar Amurka yayi a shafinsa na Tuwita @RFJ_USA, rubutun ya bayyana cewa:
"Rahoton da muka samu yau ya nuna cewa shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau, ya kashe kansa a wata fafatawa da suka yi da mayaƙan ISWAP dake biyayya ga ISIS."
Asali: Legit.ng