'Yan Sanda Sun Kame 'Yan Bindiga 4, Sun Ceto Wadanda Aka Sace 2

'Yan Sanda Sun Kame 'Yan Bindiga 4, Sun Ceto Wadanda Aka Sace 2

- Rundunar 'yan sanda a jihar Filato sun yi nasarar kame wasu bata-garin 'yan ta'adda 'yan bindiga

- Rahoto ya ce an kame mutane hudu da laifin yin garkuwa da mutane tare da kwato mutun biyu da suka sace

- Rundunar ta ce tana ci gaba da aiki don ganin ta ceto sauran mutanen da ke hannun 'yan bindigan

Mista Gabriel Ubah, jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a Filato, ya ce rundunar ta kama masu garkuwa da mutane hudu kuma ta kubutar da mutane biyu daga hannun su, The Guardian ta ruwaito.

A wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho a ranar Alhamis a karamar hukumar Mangu da ke jihar, Ubah ya ce rundunar tana kuma kokarin ceto sauran mutanen biyu da aka sace daga hannun masu garkuwar.

Ya tuna cewa masu garkuwar sun aikatata'addanci a Gaya Layout kusa da Chichim Quarters a garin Mangu da misalin karfe 8.30 na dare a ranar 19 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adama Garba

'Yan Sanda Sun Kame 'Yan Bindiga 4, Sun Ceto Wadanda Aka Sace 2
'Yan Sanda Sun Kame 'Yan Bindiga 4, Sun Ceto Wadanda Aka Sace 2 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Amma 'yan sanda da mambobin kungiyar 'yan banga sun tare su sun kame hudu daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere tare da mutum hudu da aka kashe.

A wurin da lamarin ya faru an gano harsasai 13 da ba komai a cikinsu yayin musayar wuta da jami'an tsaro.

Mista Lawrence Danat, Shugaban zartarwa na Karamar Hukumar Mangu, ya yi Allah wadai da abin da masu garkuwar suka yi, ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su tashi tsaye su yi aiki tare da ceto sauran wadanda lamarin ya rutsa da su.

Ya yaba wa jami'an tsaro a majalisar, musamman 'yan sanda da kuma kungiyar 'yan banga game da kame masu garkuwar.

'Yan sanda na ci gaba da samun nasarar kame bata-gari dake tada kayar baya a wasu sassan Najeriya.

A jihar Benue, an ruwaito yadda hukumar 'yan sanda ta yi nasarar kame wasu 'yan ta'adda sama da 130 a cikin kasa wa watanni shida wasu yankunan jihar, jaridar Leadership ta ruwaito.

Hakazalika ta kwato makamai iri daban-daban daga hannun 'yan bindigan da aka ruwaito sun haura 700.

KU KARANTA: An Kuma: 'Yan Ta'adda Cikin Kakin Soja Sun Kashe Jami'in Dan Sanda a Jihar Imo

A wani labarin na daban, Jami’an tsaro sun kubutar da wata farfesa ta Jami'ar Jos (UNIJOS), Grace Ayanbimpe da mijinta da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba dasu a Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Litinin.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an sace Farfesan da sanyin safiyar Litinin tare da mijinta. An tattaro cewa an ceto su ba tare da sun ji rauni ba.

‘Yan bindiga sun mamaye gidan ma’auratan a bayan Haske Quaters, Lamingo a karamar hukumar Jos ta Arewa inda suka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel