Shekau Gwarzo Ne: Dan Majalisa Ya Kori Mai Taimaka Masa Saboda Yabon Shekau

Shekau Gwarzo Ne: Dan Majalisa Ya Kori Mai Taimaka Masa Saboda Yabon Shekau

- Wani dan majalisar wakilai daga jihar Borno ya kori mai taimaka masa saboda yabawa Shekau

- Mai taimaka masa ya bayyana Shekau a matsayin gwarzo kuma jarumin da ya mutu gwarzo

- Wannan yasa dan majalisar ya barranta da mataimakin ya kuma aika masa da takardar kora

Abdulkadir Rahis, dan majalisar wakilai daga jihar Borno, ya kori mai taimaka masa, Bukar Tanda, saboda bayyana Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram a matsayin "gwarzo na gaskiya".

An ruwaito Shekau, ya kashe kansa da bam a ranar Laraba - don kauce wa kamun kazar kuku daga mayakan ISWAP - wani bijirarren bangare na Boko Haram.

Baana Duguri, wani kwamandan ISWAP, an nakalto yana fadar haka a cikin rahoto daga sashin leken asirin ‘yan sanda na Najeriya cewa 'yan kungiyar ta ISWAP “sun kewaye shugaban na Boko Haram tare da tawagarsa sannan kuma an yi harbe-harbe tsakanin bangarorin biyu”.

KU KARANTA: Cece-Kuce Yayin da Wasu Gwamnoni Suka Halarci Biki Maimakon Jana'izar Janar Attahiru

Shekau Gwarzo Ne: Dan Majalisa Ya Kori Mai Taimaka Masa Saboda Yabon Shekau
Shekau Gwarzo Ne: Dan Majalisa Ya Kori Mai Taimaka Masa Saboda Yabon Shekau Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Amma a wani sakon da ya wallafa a Facebook a ranar Alhamis, Tanda ya yaba wa shugaban Boko Haram din, yana mai cewa "ya yi rayuwa irin ta gwarzo kuma ya mutu gwarzo na gaskiya".

“Ina matukar yabawa da kuma gamsuwa da kwarin gwiwarsa na kawo karshen rayuwarsa. Ya yi rayuwar jarumi kuma ya mutu gwarzo na gaske. Ya yi hakan ne ta yadda ba za a gano ko gawarsa ba,” in ji Tanda, TheCable ta ruwaito.

Kalaman ba su yi wa Rahis dadi ba, wanda ya dankara masa kora ta hanyar ba shi doguwar takarda.

"Ina so na rubuta a hukumance tare da sanar da kai game da dakatar da nadin ka a matsayin mai taimaka min kan harkokin doka, nan take," in ji Rahis a wata wasika da shi da kan sa ya sanya hannu.

“Ayyukanka, furucinka da ra’ayinka na kwanan nan sun banbanta da ra’ayina, na mazabata da babbar jam’iyyarmu, APC.

"Har ila yau wasikar ta zama barranta ga duk wani mataki ko matsayi da ka dauka ko kake son dauka, a kan duk wani lamari da ka iya kasancewa yana da kusanci da ni a karan kai na ko ofishi na.”

Shekau ya kasance yana aikata ta'addanci a yankin arewacin Najeriya fiye da shekaru goma.

KU KARANTA: Kada Mutuwar Janar Attajiru Ta Kashe Muku Kwarin Gwiwa, IGP Ga Sojojin Najeriya

A wani labarin, Mata da yara masu kananan shekaru na daga cikin mayakan da suka yi artabu da Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, a daya daga cikin fadace-fadace mafi muni da yayi a rayuwarsa.

Wasu majiyoyi game da harin sun shaida wa Daily Trust cewa ISWAP ta yi amfani da mayaka 'yan tsakanin shekara 12 zuwa 30 a harin.

An ce duka bangarorin sun yi asara a artabun amma sansanin na Shekau ya fi yin asara yayin da shugaban ya yi kunar bakin wake ya kashe kansa ko kuma ya samu munanan raunuka da suka sa da wuya ya rayu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel