COVID19: Mutum 60,000 Kacal Saudiyya Ta Amince Zasu Yi Hajjin Bana a Duniya
- Saudiyya ta bayyana cewa mutum 60,000 kacal ta amince du gudanar da aikin hajjin bana a faɗin duniya
- Ƙasar tace 15,000 daga ciki zasu fito ne daga ƙasar Saudiyya, yayin da 45,000 daga sauran ƙasashen duniya
- Saudiyya ta dakatar da gudanar da aikin hajji a bara sabida ɓarkewar cutar COVID19 a duniya
Ƙasar saudiyya ta bayyana adadin mahajjatan da zasu samu damar yin aikin hajji a wannan shekarar ta 1442 byan hijira, wacce tazo dai-dai da 2021.
KARANTA ANAN: Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah
Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da hukumar hajji ta ƙasa ta futar a shafiɓta na dandalin sada zumunta facebook 'National Hajj Commission Of Nigeria.'
Saudiyya tace adadin mutane 60,000 ne zasu samu izinin gudanar da aikin hajji a faɗin duniya baki ɗaya.
Daga cikin wannan adadin, 15,000 zasu fito ne daga cikin ƙasar ta Saudi Arabia yayin da ragowar 45,000 za'a rarrabawa ƙasashen duniya.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Naɗa Sabon Hakimin Kanƙara
Hakanan hukumomin ƙasar sun fitar da dokoki dake ƙunshe da dukkan bayanan yadda aikin hajjin zai gudana.
Idan baku manta ba Saudiyya ta dakatar da gudanar da aikin hajji ne sabida guje wa yaɗuwar cutar COVID19.
A wani labarin kuma Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike
Hukumar binciken haɗurra ta ƙasa AIB-N, ta bayyana cewa ta gano wani baƙin akwati na jirgin da yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojin Najeriya, Ibrahim Attahiru da wasu jami'ai 10.
Hukumar tace ta gano FDR da CVR waɗanda ke naɗar bayanai da murya yayin da jirgi ke tafiya a sararin sama, ta kuma tabbatar da cewa zata gudanar da bincike mai tsanani.
Asali: Legit.ng