Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Naɗa Sabon Hakimin Kanƙara

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Naɗa Sabon Hakimin Kanƙara

- Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya naɗa sabon hakimin Kanƙara

- Wannan ya faru ne bayan tsige wancan da majalisar sarkin tayi inda ta kama shi da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa yan bindiga

- Sarkin ya naɗa Justice Adamu Bello a matsayin wanda zai maye gurbin kujerar sarkin Pauwan Katsina, Hakimin Kanƙara

Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya naɗa sabon sarkin Pauwan Katsina, Hakimin Kanƙara.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga

Wannan na zuwa ne bayan sarkin ya tsige tsohon hakimin, Alhaji Yusuf Lawal, bayan gano cewa yana taimaka wa yan bindigan da suka addabi jihar.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Naɗa Sabon Hakimin Kanƙara
Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Naɗa Sabon Hakimin Kanƙara Hoto: Katsina Daily Post FB Fage
Asali: Facebook

Sarkin ya naɗa Justice Adamu Bello a matsayin wanda zai maye gurbin Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kanƙara.

KARANTA ANAN: Hukumar AIB Ta Gano Wani Muhimmin Akwati a Hatsarin Jirgin COAS Attahiru, Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Bincike

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da Katsina Daily Post ta wallafa a shafinta na kafar sada zumunta Facebook.

Rahoton naɗin ya bayyana cewa Sarkin Labaran Majalisar sarkin Katsina, shine ya tabbatar da wannan sabon naɗin da sarki yayi.

Legit.ng hausa ta kawo muku rahoto cewa bayan gano tsohon hakimin Kankara na da hannu a hare-haren yan Bindiga, majalisar sarkin ta yanke shawarar tumɓuke shi daga muƙaminsa.

A wani labarin kuma Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Ofishin gwamnatin Amurka a Najeriya ya jajantawa yan Najeriya a kan rasuwar shugaban soji tare da wasu sojoji 10 a haɗarin jirgi.

Shugaba Rundunar soji, Ibrahim Attahiru, tare da wasu mutum 10 sun rasa rayuwarsu a hatsarin jirgi ranar Jumu'a 21 ga Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262