IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu

IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu

- Sufetan yan sanda na ƙasa (IGP), Usman Baba, ya musanta zargin cewa hukumar tasan za'a kawo hari a Abuja da Plateau

- Sefetan ya bayyana haka ne a wani saƙo da kakakin hukumar yan sanda, Mr. Frank Mba, ya fitar yau a Abuja

- Ya roƙi jama'ar dake zaune a Abuja da jihar Plateau su kwantar da hankalinsu kuma su cigaba da tafiyar da rayuwarsu yadda suka saba

Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, yace babu wani abun tsoro kan barazanar kawo hari Abuja da Plateau, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba

Kakakin hukumar yan sanda, Mr Frank Mba, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar ranar Juma'a a Abuja, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta gano wani rahoton sirri dake nuni da cewa, sufetan yan sanda ya baiwa kwamishinan Plateau da takwaransa na Abuja umarnin su ɗauki matakin da ya dace domin daƙile duk wani hari da za'a kawo yankunan su.

IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu
IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

IGP ya roƙe su da su kare muhimman kayayyakin gwamnati dake yankin su biyo bayan gano shirin mayaƙan Boko Haram na kai hari.

Sai dai kakakin hukumar yan sandan ya bayyana cewa wannan umarnin ba yana nufin akwai wata barazanar kawo hari a biranen biyu bane.

KARANTA ANAN: UNIJOS Ta Umarci Ɗalibai Subar Ɗakunan Kwanan Su Cikin Gaggawa Saboda Wani Muhimmin Dalili

Yace an baiwa kwamishinonin biyu umarnin ne don su ƙara shiri wajen dakile duk wata barazanar kawo hari daga yan ta'adda a yankunan su.

A cewarsa, anyi hakan ne don a ƙara tabbatar da doka a waɗannan garuruwan kuma a kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu.

"Umarnin ba yana nufin an san cewa za'a kawo hari a jihohin biyu bane kamar yadda wasu ke yaɗa wa." inji kakakin yan sandan.

Ya kuma roƙi mazauna waɗannan jihohin biyu su kwantar da hankalinsu, su cigaba da gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

A wani labarin kuma Karin Bayani: Rundunar Soji Tayi Magana Kan Mutuwar Shugaban Boko Haram Abubakar Sheƙau

Rundunar sojin ƙasar nan tayi magana kan rahoton dake nuna cewa shugaban Mayaƙan Boko Haram, Abubakar Skeƙau, ya sheƙa lahira.

Sojin sun ce a halin yanzun ba zasu iya tabbatar da labarin ba amma suna cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262