Karin Bayani: Rundunar Soji Tayi Magana Kan Mutuwar Shugaban Boko Haram Abubakar Sheƙau
- Rundunar sojin ƙasar nan tayi magana kan rahoton dake nuna cewa shugaban Mayaƙan Boko Haram, Abubakar Skeƙau, ya sheƙa lahira
- Sojin sun ce a halin yanzun ba zasu iya tabbatar da labarin ba amma suna cigaba da gudanar da bincike kan lamarin
- Rahoton dai ya bayyana cewa Sheƙau ya rasa ransa ne yayin da abokan hamayyarsu ISWAP suka kai musu hari a dajin Sambisa
Rundunar soji tace har yanzun bata samu ingantaccen bayani kan rahoton mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau ba.
Wani rahoton bincike ya bayyana cewa Sheƙau ya mutu ne a wata fafatawa da suka yi da mayaƙan dake fafutukar kafa kasar musulunci a nahiyar Afirca (ISWAP).
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Damƙa Sabbin Jiragen Yaƙi Uku Ga Rundunar Sojin Sama
Rahoton ya bayyana cewa, Abubakar Shekau yaji mummunan rauni yayin da yayi ƙoƙarin kashe kansa don kada abokan hamayyarsa ISWAP su kama shi a wata fafatawa da suka yi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Rahoton ya kuma bayyana cewa shugaban Boko Haram ɗin ya sheƙa lahira bayan jiwa kansa mummunan rauni, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ahmad Lawan Ya Caccaki Masu Sukar Majalisa, Ya Nemi Yan Najeriya Su Musu Adalci
A wata tattaunawa da dailytrust tayi da ƙwararre a ɓangaren tsaro, Kabiru Adamu, yace ko an kashe shakau ko yana raye, ISWAP na ƙara ƙarfi idan ka duba irin ayyukan d suke yi a yanzun.
Yace: "Abinda wannan rahoton ke nuna wa rundunar soji shine sun bar ISWAP ta ƙara ƙarfi a ɓangaren kai hare-haren su, kuma wannan mummunan saƙo ne suke aikewa ƙungiyoyin ta'addanci."
"Wannan saƙon na nuna wa mutanen dake shiga rundunar soji da waɗannan ƙungiyoyi cewa gara su shiga waɗannan ƙungiyoyin na ta'addanci saboda sunfi rundunar soji ƙarfi.
Da aka tuntuɓi daraktan yaɗa labarai na rundunar, Brig.-Gen. Bernard Onyeuko, ya faɗawa manema labarai ta hanyar tura saƙo cewa bashi da bayani akan rahoton.
"Kuyi hakuri, bani da bayani akan haka." inji shi.
A wani labarin kuma El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba
Gwamnan Kaduna , Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ya kamata Najeriya ta daina dogara da albarkatun man fetur.
Gwamnan yace akwai hanyoyi da dama da za'a iya bi domin tattara bayanan kowane ɗan Najeriya sannan a sanya mishi haraji.
Asali: Legit.ng