Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba

Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba

- Ƙasar Amurka tayi magana kan rahoton dake yawo cewa shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau, ya sheƙa lahira

- Sashin shari'a na ƙasar Amurka ya bayyana cewa ba zasu baiwa ƙungiyar ISWAP tukuicin da suka sa kan duk wanda ya kawo bayanan inda Sheƙau yake

- Tun shekarun baya ƙasar Amurka ta saka sunan Abubakar Sheƙau a cikin jerin sunayen yan ta'addan duniya

Ƙasar Amurka ta bayyana cewa ƙungiyar ISWAP ba zata samu ko sisi ba daga cikin dala miliyan $7m data sa kan duk wanda ya gano inda Abubakar sheƙau yake.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Rundunar Soji Tayi Magana Kan Mutuwar Shugaban Boko Haram Abubakar Sheƙau

Yayin da take martani kan rahoton mutuwan shugaban mayaƙan Boko Haram ɗin, Amurka tace ba zata baiwa ƙungiyar dake ƙarƙashin ISIS ba.

Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba
Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba Hoto: ndtv.com
Asali: UGC

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da sashin shari'a na ƙasar Amurka yayi a shafinsa na Tuwita @RFJ_USA, rubutun ya bayyana cewa:

"Rahoton da muka samu yau ya nuna cewa shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau, ya kashe kansa a wata fafatawa da suka yi da mayaƙan ISWAP dake biyayya ga ISIS."

"Baku cancanci tukuicin da muka sa ga wanda ya bada bayanan inda yake ba, haka shirin namu ya ƙunsa."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Ta Goyi Bayan Gwamnonin Kudu Kan Hana Kiwo

Legit.ng hausa ta gano cewa a ranar 21 ga watan Yuni, 2012, sashin shari'a na ƙasar Amurka ya bayyana shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau, a matsayin ɗaya daga cikin yan ta'addan duniya.

Bayan shekara daya da saka sunan Abubakar sheƙau, sashin ya sanya tukuicin dala miliyan $7m ga duk wanda ya kawo bayanan inda maɓoyarsa take.

A wani labarin kuma Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adamu Garba

Adamu Garba, wani tsohon dan takarar shugaban kasa ya bayyana jin dadinsa ga mutuwar Shekau.

Dan takarar ya ce, mutuwar Shekau ya kamata ta zama darasi ga Sunday Igboho da Nnamdi Kanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262