UNIJOS Ta Umarci Ɗalibai Subar Ɗakunan Kwanan Su Cikin Gaggawa Saboda Wani Muhimmin Dalili

UNIJOS Ta Umarci Ɗalibai Subar Ɗakunan Kwanan Su Cikin Gaggawa Saboda Wani Muhimmin Dalili

- UNIJOS ta umarci ɗaliban ta dake zaune a ɗakin kwanan ɗalibai da su bar wajen cikin gaggawa saboda wani rahoto da suka samu na tsaro

- Jami'ar ta bayyana cewa wannan umarnin ya shafi dukkan ɗaliban dake karatun digiri na farko da na biyu

- Wasu ɗalibai dake karatu a makarantar sun tabbatar da wannan matakin da Jami'ar su ta ɗauka

Jami'ar Jos (UNIJOS) ta baiwa ɗaliban dake zaune a ɗakin kwanan makarantar da su bar wajen cikin gaggawa.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba

A wani jawabi da sakataren majalisar ƙoli ta makarantar, Monday Danjem, ya sawa hannu kuma aka fitar dashi ta shafin facebook ɗin mataimakinsa, Abdullahi Abdullahi, ya bayyana cewa sun yanke wannan hukuncin ne gaba ɗayan su.

Jawabin ya cigaba da cewa ɗakin kwanan zai cigaba da kasancewa a kulle saboda wani rahoton tsaro da jami'ar ta samu daga kwamishinan yan sandan jihar Flato.

UNIJOS Ta Umarci Ɗalibai Subar Ɗakunan Kwanan Su Saboda Wani Muhimmin Dalili
UNIJOS Ta Umarci Ɗalibai Subar Ɗakunan Kwanan Su Saboda Wani Muhimmin Dalili Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Rundunar Soji Tayi Magana Kan Mutuwar Shugaban Boko Haram Abubakar Sheƙau

Jawabin yace: "Mun yanke wannan hukuncin ne bayan shawarwarin ɗa muka samu a taron da mukayi da ƙungiyar ɗalibai, kwamishinan yan sanda, da sauran hukumomin tsaro."

"Mun faɗa wa ɗaliban su yi hakuri a baiwa hukumomin tsaro sati biyu domin su gudanar da bincike kan yanayin da ake ciki."

"Hakanan kuma an dakatar da lakcar ɗaliban dake karatun digiri na farko a zangon karatu na biyu har sai ranar 7 ga watan Yuni 2021. Amma ɗalibai masu karatun digiri na biyu zasu cigaba da gudanar da al'amuran karatunsu."

Da yawa daga cikin ɗaliban makarantar sun bayyana cewa an basu umarnin su bar ɗakin kwanan su cikin gaggawa.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Damƙa Sabbin Jiragen Yaƙi Uku Ga Rundunar Sojin Sama

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da shigar da sabbin jiragen yaƙi uku zuwa cikin kayan aikin NAF.

Shugaban wanda ministan tsaro, Bashir Magashi, ya wakilta, yace wannan babbar nasara ce da gwamnatinsa ta samu na cika alƙawarin da ta ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262