Matawalle Ya Bada Umurnin Rufe Kasuwanni Huɗu a Zamfara

Matawalle Ya Bada Umurnin Rufe Kasuwanni Huɗu a Zamfara

- Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya bada umurnin rufe wasu kasuwani hudu a jiharsa

- Matawalle ya ce an dauki wannan matakin ne domin inganta tsaro da tabbatar da doka da oda

- Har wa yau, gwamnan na Zamfara ya kuma umurci a kwace dukkan takardun izinin mallakar filaye a jihar

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bada umurnin rufe kasuwanni hudu a kananan hukumomi biyu a jihar da ke yankin arewa maso yamma na Nigeria, Channels Television ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, Bala Maru ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, yana mai cewa dokar za ta fara aiki nan take.

Matawalle Ya Bada Umurnin Rufe Kasuwanni Huɗu a Zamfara
Matawalle Ya Bada Umurnin Rufe Kasuwanni Huɗu a Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zamfara: Dole Manoma Su Fara Aiki a Gonakinmu Kafin Nasu, Dogo Giɗe da Black

Ya yi bayanin cewa hakan ya zama dole ne domin kiyayye doka da oda a biranen da kauyukan da abin ya shafa da makwabtansu.

A cewar sanarwar, uku daga cikin kasuwannin da dokar ya shafa suna karamar hukumar Birnin Magaji sannan na hudun yana karamar hukumar Maru.

Kasuwannin sun hada da na Sabon Birni da ake ci a ranakun Alhamis, Cigama da ake ci a ranar Juma'a da Kokiya da ake ci a ranar Talata dukkansu a Birnin Magaji, da kuma kasuwar Dansadau da ake ci a ranar Juma'a a Maru.

Kazalika, Gwamna Matawalle ya bada umurnin kwace takardun dukkan filayen da ke jihar.

KU KARANTA: Zagin Buhari Sakarci Ne, Umahi Ya Ja Kunnen Matasan Kudu

Ya bukaci masu filayen su tafi hukumar kula da filaye da sufiyo ta jihar domin sake jadada takardun filayen nasu da sabon tsari na zamani.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne yayin kaddamar da bada shaidan mallakar fili na zamani (e-C of O), yana mai cewa hukumar ta ZAGIS ce kawai za ta iya tantance filayen.

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel