Inda ni na sha ban-bam da sauran masu mulki da ‘yan siyasar kasar nan inji Shugaba Buhari

Inda ni na sha ban-bam da sauran masu mulki da ‘yan siyasar kasar nan inji Shugaba Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan harkar zabe a Najeriya

- Buhari ya yi wannan bayani ne da ya zauna da wasu ‘Yan Najeriya a Faris

- Shugaban kasar yace gwamnatinsa da gaske take kan shirya zaben gaskiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa da gaske ta ke yi wajen ganin an gudanar da zabuka na gaskiya, kuma masu nagarta.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya yarda kowane ‘dan kasa yana da damar da zai zabi duk wanda yake so a matsayin shugabansa.

Jaridar The Cable ta rahoto shugaban kasar yana cewa mutane sun saba yin ‘a mutu-ko-a yi rai’ domin ganin sun samu kujerar siyasa a kasar nan.

KU KARANTA: Rikici na jiran APC a kan yunkurin daga lokacinzaben jam’iyya

Muhammadu Buhari ya ce zai yi kokari wajen ganin bai yi katsalandan a kan sha’anin zabe ba. Jaridar Premium Times ta fitar da irin wannan rahoto.

Buhari yake cewa duk abin da ‘yan siyasa suke yi na ganin sun samu mulki, shi ba haka yake yi ba, ya ce wannan ne ma ya sa ya fadi zabuka a baya.

A ranar Laraba, 19 ga watan Mayu, 2021, shugaban Najeriyar ya yi wannan bayani a lokacin da yake zanta wa da wasu ‘Yan Najeriya a kasar Faransa.

Shugaban kasar yake cewa damukaradiyya ba zai tafi ba, ba tare da an ba jama'a damar su dauki zabi ba.

KU KARANTA: Kwamitin NGF/El-Rufai yana so fetur ya tashi daga N165 zuwa N408

Inda ni na sha ban-bam da sauran masu mulki da ‘yan siyasar kasar nan inji Shugaba Buhari
Buhari da Osinbajo Hoto: BBC/EPA
Asali: UGC

“Gudanar da zaben gaskiya na gari abin damuwa ne. A zabukan da aka yi a baya, jam’iyyarmu ta sha kashi a wasu wuraren, hakan ya nuna adalcinmu.”

“An saba, wadanda ke kan mulki, suna kokarin su ci zabe da karfi da yaji. Mun yi imani da ingantaccen zabe, na gaskiya.” Inji Muhammadu Buhari.

“Mun ba jami’an tsaro umarni su yi maganin duk mai amfani da ‘yan daba domin kawo matsala.” Buhari ya na mai shan alwashin ganin an gyara zaben kasar.

A ranar Laraba ne ku ka ji cewa 'yan Majalisar wakilan tarayya za su wajabtawa Shugaban Najeriya nada Ministoci a cikin kwana 30 da rantsar da shi.

Za a tursasawa shugabanni kafa Gwamnatinsu wata daya da hawa mulki ko a sauke su. Idan kudirin ya zama doka, zai karawa 'yan majalisar kasar karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel