Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Ceto Farfesan UNIJOS da Mijinta Daga 'Yan Bindiga

Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Ceto Farfesan UNIJOS da Mijinta Daga 'Yan Bindiga

Jami’an tsaro sun kubutar da wata farfesa ta Jami'ar Jos (UNIJOS), Grace Ayanbimpe da mijinta da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba dasu a Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Litinin.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an sace Farfesan da sanyin safiyar Litinin tare da mijinta.

An tattaro cewa an ceto su ba tare da sun ji rauni ba.

‘Yan bindiga sun mamaye gidan ma’auratan a bayan Haske Quaters, Lamingo a karamar hukumar Jos ta Arewa inda suka yi awon gaba da su.

Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Ceto Farfesan UNIJOS da Mijinta Daga 'Yan Bindiga
Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Ceto Farfesan UNIJOS da Mijinta Daga 'Yan Bindiga Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Filato, Ubah Ogaba, wanda ya tabbatar da hakan ya ce:

"Tare da hadin kai da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda da ke Jihar Filato, Mafarauta da 'yan banga, wadanda aka yi garkuwar da su Farfesa Grace Ayanbimpe da mijinta Mista Isaac Ayanbimpe an ceto su ba tare da rauni ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel