An Kuma: 'Yan Ta'adda Cikin Kakin Soja Sun Kashe Jami'in Dan Sanda a Jihar Imo
- Wasu 'yan ta'adda sun hallaka jami'in dan sanda a wani yankin jihar Imo a kudancin Najeriya
- Rahoto ya bayyana cewa, 'yan ta'addan sun yi shiga cikin kakin soja sadda suka hallaka jami'in
- Ana ci gaba da hallaka jami'an tsaro a yankin kudu, lamarin da ya jawo tashin hankali a kasar
A jiya ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga cikin kakin soji sun kashe wani jami’inta, Sajan Loveday Obilonu, a hanyar Okwu Uratta da ke Owerri, jihar Imo, Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Abutu Yaro, ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri, ta bakin jami’in hulda da jama’a na yan sanda na jihar, Bala Elkana.
Abutu ya ce Sajan Loveday na daga cikin jami'an da aka tura don kare 'yan jihar daga masu aikata laifuka.
KU KARANTA: Jami'an Kwastam Ta Kame Motar Dangote Makare da Haramtacciyar Shinkafar Waje
A bincikensu na farko, ya kara da cewa wasu ‘yan bindigan sun kashe jami’in ne bayan da suka gane shi dan sanda ne kuma yana dauke da bindiga.
Duk da haka, rundunar ‘yan sanda ta Imo ta ce ta fara gudanar da bincike don kamo wadanda suka aikata aika-aikar.
A yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu, tsageru na ci gaba da kashe jami'an tsaro da kuma kone-konen ofisoshin jami'an tsaro.
A farkon shekerar nan, wasu ‘yan daba sun kai hari ofishin yan sanda na Umuoba da ke karamar hukumar Isiala Ngwa ta Arewa a jihar Abia a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu inda suka kashe wani sifeton ‘yan sanda, Premium Times ta ruwaito.
Wani rahoton jaridar Punch, ya bayyana yadda aka yi asarar jami'an tsaro sama da 120 tare da kone-konen ofisoshin hukumonin tsaro na 'yan sanda da gidan yari.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: ISWAP Sun Afkawa Mafakar Boko Haram, Ana Kyautata Zaton Shekau Ya Mutu
A wani labarin, Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Benue sun kama wasu mutane 131 da ake zargi da aikata laifi a fadin jihar. Ana zarginsu da aikata laifuka da suka hada da satar mutane, fashi da makami da kuma barna ta kungiyar asiri.
‘Yan sanda sun kuma kwato makamai daban-daban guda 785 daga hannun su.
Wannan ya kasance ne kamar yadda rundunar ta kuma bai wa jami'anta guda bakwai, wadanda suka yi fice a fagen ayyukansu kyautuka na kwarai.
Asali: Legit.ng