Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adamu Garba

Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adamu Garba

- Adamu Garba, wani tsohon dan takarar shugaban kasa ya bayyana jin dadinsa ga mutuwar Shekau

- Dan takarar ya ce, mutuwar Shekau ya kamata ta zama darasi ga Sunday Igboho da Nnamdi Kanu

- Ya kuma ce, haushinsa daya, ya kamata ace jefe Shekau aka yi ya mutu har lahira a bainar jama'a

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba, ya ce shugaban kungiyar Biafra, Nnamdi Kanuda kuma dan rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Igboho, ya kamata su dauki darasi a labarin da aka ruwaito na mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Wani dandalin yanar gizo, HumAngle, ya ruwaito cewa Shekau ya mutu a yammacin Laraba bayan mamayar kungiyar ISWAP yankin dajin Sambisa ta yi wa mafakar Boko Haram.

Shekau, wanda ya sanya rigar kunar bakin wake, an ruwaito cewa ya tarwatsa kansa tare da duk wanda ke wurin yayin wata tattaunawa.

KU KARANTA: An Kuma: 'Yan Ta'adda Cikin Kakin Soja Sun Kashe Jami'in Dan Sanda a Jihar Imo

Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adama Garba
Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adama Garba Hoto: globalnewsng.com
Asali: UGC

Shekau ya kasance shugaban kungiyar Boko Haram tun shekara ta 2009 biyo bayan mutuwar wanda ya kafa kungiyar, Mohammed Yusuf.

Kafin lamarin na yau, an yi ta yayatawa cewa an kashe shi a lokuta daban-daban.

Da yake mai da martani, a wani sakon da ya wallafa a ranar Alhamis, Garba ya ce zai fi so a jefe Shekau har lahira.

Ya rubuta a shafin Tuwita cewa:

“Damuwa ta kawai da mutuwar Shekau shi ne samun 'yancin zabar yadda ya mutu.

"Yakamata 'yan gari su jefeshi har lahira a dandalin Kasuwar Doron Baga akan TV kai tsaye, karkashin kulawar Sojojin Najeriya kowa ya gani.

"Hakan zai aika sako ga Kanu da Igboho."

KU KARANTA: Jami'an Kwastam Ta Kame Motar Dangote Makare da Haramtacciyar Shinkafar Waje

A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya tace ta fara binciken rahoton dake nuna cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau, yaji mummunan rauni kuma ya mutu.

Wani rahoto ya bayyana cewa, Abubakar Shekau yaji mummunan rauni yayin da yayi ƙoƙarin kashe kansa don kada abokan hamayyarsa ISWAP su kama shi a wata fafatawa da suka yi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Rahoton ya kuma bayyana cewa shugaban Boko Haram ɗin ya sheƙa lahira bayan jiwa kansa mummunan rauni, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel