Jerin lokuta biyar da aka rahoto cewa Shugaban Boko Haram Shekau ya mutu
Rahoton baya-bayan nan da ke nuna cewa Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram ya mutu ba shine karo na farko da ake fada wa ’yan Najeriya cewa an kashe dan ta’addan da ya addabi al’umma ba.
Kamar dai sauran lokuta, akwai ikirari da ba a tabbatar da su ba a ranar Laraba, 19 ga Mayu, cewa an kashe Shekau a yayin artabu da mambobin kungiyar Islamic State West Africa (ISWAP) a cikin dajin Sambisa.
Fiye da shekaru goma, labarai sun yawaita game da zargin kisan dan ta’addan da kuma yadda yake sake bayyana da karin karfi da kayayyaki don ci gaba da aikinsa na addabar yan Najeriya, musamman a yankin arewa maso gabas.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki
1. 2009
A shekarar 2009, An yi ta maganganu game da mutuwarsa sakamakon mummunan hari da sojoji suka kaddamar. Kodayake an yi ikirarin cewa harin ya murkushe masu tayar da kayar baya da yawa a lokacin, amma Shekau ya sake bayyana a yanar gizo, a wannan karon a matsayin sabon shugaban kungiyar, BBC Pidgin ta ruwaito.
2. 2013
Shekaru hudu bayan nan, rahotanni sun ce Shekau ya samu munanan raunuka daga harsasai a lokacin artabu da sojojin Najeriya a watan Agusta, kawai sai ga shi ya bugi kirji a watan Satumba cewa ba a kashe shi ba.
KU KARANTA KUMA: Ahmed Musa na shirin barin Kano Pillars a watan Yuni, ya yi jinjina ta musamman ga Ali Rabiu
3. 2014
Bai tsaya a nan ba, wani ikirari da majiyoyin Sojojin Najeriya suka yi wanda ya samu goyon bayan wasu mutane daga rundunar sojan Kamaru sun ce da gaske ne mai laifin da ake nema ya mutu a Kodunga yayin yakin kwana biyu. Sai dai kuma, ya fito ya karyata labarin.
4. 2015
A shekarar 2015, Shekau cikin alfahari ya karyata rahoton da marigayi shugaban Chadi, Idriss Derby ya gabatar a baya cewa sabon shugaban kungiyar ta’addacin ya bayyana bayan zargin mutuwarsa.
5. 2016
A shekarar da ta biyo baya, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ba da sanarwar cewa an kashe mai dan ta’addan tare da wasu jiga-jigan kungiyar Boko Haram a Borno. Wannan kuma bai zama gaskiya ba kamar yadda aka ganshi ba da daɗewa ba a cikin bidiyon Youtube yana barazanar tada zaune tsaye.
A halin da ake ciki, mun ji cewa wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa. In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito.
Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.
Wasu majiyoyi sun ce daruruwan mayakan ISWAP sun mamaye Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau wanda shi ne shugaban kungiyar Boko Haram.
Asali: Legit.ng