Rahoto: Akalla jami'ai 127 Aka Kashe a Yankunan Kuduncin Najeriya, An Kona Ofisoshi 25

Rahoto: Akalla jami'ai 127 Aka Kashe a Yankunan Kuduncin Najeriya, An Kona Ofisoshi 25

Rahoto ya bayyana yadda gwamnatin Najeriya ta yi asarar jami'anta da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro sakamakon hare-haren 'yan ta'adda a yankunan kudu maso gaba da kudu maso kudancin kasar.

Fiye da ofisoshin ‘yan sanda 25 aka kai wa hari a sassan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a cikin watanni biyar da suka gabata.

Rahotannin sun kuma nuna cewa an kashe ‘yan sanda sama da 127 da sauran jami’an tsaro yayin hare-haren.

Hare-haren da suka faru a jihohin Abia, Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi, Kuros Riba da jihar Ribas, sun yada tsoro tsakanin jama'a.

An tattaro cewa jami'an tsaro da yawa na neman sauya wuraren aiki zuwa sassan da ba su da tashin hankali, a rahoton jaridar Punch.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma a Kaduna

Rahoto: Akalla jami'ai 127 Aka Kashe a Yankunan Kuduncin Najeriya, An Kona Ofisoshi 25
Rahoto: Akalla jami'ai 127 Aka Kashe a Yankunan Kuduncin Najeriya, An Kona Ofisoshi 25 Hoto: thisnigeria.com
Asali: UGC

A kasa da mako guda, a ranar Litinin da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kona Ofishin 'yan sanda na Apumiri Ubakala a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mista Geoffrey Ogbonna, wanda ya tabbatar da harin, ya ce an kashe 'yan sanda biyu yayin harin, The Guardian ta ruwaito.

Harin wanda ya afku duk da dokar hana fita daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe da aka sanya wa sassan jihar, shi ne na biyar cikin kwanaki takwas.

Kafin kai harin, an kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda na Nkporo, Uzuakoli, Ubani Ibeku da Bende tare da kone su.

Tun da farko a ranar 23 ga watan Janairu, an kashe ‘yan sanda biyu bayan da wasu 'yan bindiga suka mamaye wani ofishin ‘yan sanda a garin Aba.

A ranar 1 ga watan Fabrairu, wasu ‘yan daba wadanda yawansu ya kai 20 sun yi kaca-kaca da rundunar 'yan sanda a Omoba, a karamar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu da ke jihar Abia, inda suka kashe wani dan sanda tare da kwasar ganimar wurin ajiyar makamai.

‘Yan bindigar sun kuma kai hari ofishin 'yan sanda na Abayi da ke karamar Hukumar Osisioma Ngwa a Abia a ranar 23 ga watan Fabrairu, sun kashe wani dan sanda, sun kwaci ganima tare da cinna wa ofishin wuta.

A ranar 23 ga watan Maris, an kashe wasu ’yan sanda uku da ke aiki a sashin 'yan sanda na Abiriba a karamar hukumar Ohafia sannan aka tafi da bindigoginsu. Hakazalika, an kona wani ofishin ‘yan sanda a karamar hukumar Ihitte-Uboma a ranar 9 ga watan Maris.

A jihar Imo, an kashe ‘yan sanda biyu a ranar 5 ga watan Fabrairu a ofishin 'yan sanda na Umulowo da ke karamar hukumar Obowo.

Haka kuma an harbi wata ‘yar sanda lokacin da wasu da ake zargin 'yan daba ne suka kai hari ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Aboh Mbaise a ranar 25 ga Fabrairu.

A ranar 5 ga Afrilu, wasu ‘yan bindiga sun kai hari hedikwatar rundunar 'yan sanda ta Jihar Imo da kuma gidan yari dake Owerri. Sun wawushe rumbunan ajiyar makamai, sun kone motoci da yawa kuma sun saki akalla wadanda aka tsare 600 da fursunoni 1,844.

'Yan daban sun kuma kai hari kan hedkwatar 'yan sanda da ke Isiala Mbano a ranar 20 ga watan Maris, amma ba a samu asarar rai ba.

A jihar Anambra, wasu 'yan ta'adda sun kashe wani jami'in dan sanda tare da kone motar sintiri a Ekwulobia a ranar 24 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA: A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari cikin garin Batsari da ke Katsina

A ranar 18 ga watan Maris, an kashe wasu ‘yan sanda da ba a tantance adadinsu ba a Ekwulobia lokacin da 'yan bindiga suka kai hari wurare daban-daban. An kashe wasu ma’aikatan Hukumar Kula da gidan yari a Awka, wadanda ke rakiyar fursunoni zuwa kotu a Ekwulobia.

A ranar 31 ga watan Maris, an kashe ’yan sanda uku da ke aiki tare da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Farfesa Charles Soludo a Isuofia.

An sake samun irin wadannan munanan hare-hare a jihar Ebonyi lokacin da aka kai wa ’yan sanda uku hari a ofishin 'yan sanda na Onueke da ke karamar Hukumar Ezza ta Kudu ta jihar a ranar 8 ga watan Janairu.

An kona wani ofishin ‘yan sanda a Isu, karamar hukumar Onicha a ranar 4 ga watan Fabrairu, a ranar 1 ga watan Maris, an kai wa ofishin 'yan sanda hari a ofishin ‘yan sanda na Iboko da ke Izzi.

A ranar 14 ga Afrilu, an kashe 'yan sanda uku da ke cikin tawagar 'yan sanda na Safer Highway Patrol a wani hari da aka kai a kan titin Ogoja zuwa Abakaliki da ke kusa da mahadar Nwaezenyi.

Maharan, wadanda suka yi shigar burtu kamar za su jana’iza, sun bude wuta lokacin da aka tsayar da su domin bincike.

Mataimakin Sufeto-Janar fannin Ayyuka, Johnson Kokumo, a wani taron tattaunawa a Abuja a watan Afrilu ya ce an kashe sama da ‘yan sanda 20 a fadin kasar zuwa watan Maris.

Wani kwararre kan leken asiri da hatsarin tsaro, Kabir Adamu, ya koka kan harin da aka kai wa jami'an tsaro da kuma cibiyoyin tsaro.

Adamu ya ce, “Wannan manuniya ce cewa abin da muka hango na iya faruwa. Lokacin da 'yan bindiga suka fara kai hare-hare kan rukunin sojoji a Kudu maso Gabas, akwai wani bincike da ya nuna cewa share fage ne ga wani babban shiri da suke da shi.

"Kuma wannan shirin na iya hadawa da kai harin bai daya ta wannan hanyar, kuma sakamakon abin da ya faru, bana tunanin Najeriya zata iya jure wani rikicin bai daya kamar abinda ke faruwa a yankin Arewa maso gabas ba.”

KU KARANTA: Wabba: El-Rufai Ya Yi Hayar 'Yan Daba Cike Da Manyan Motoci 50 Su Fatattaki NLC

A wani rahoton na daban, Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Benue sun kama wasu mutane 131 da ake zargi da aikata laifi a fadin jihar. Ana zarginsu da aikata laifuka da suka hada da satar mutane, fashi da makami da kuma barna ta kungiyar asiri.

‘Yan sanda sun kuma kwato makamai daban-daban guda 785 daga hannun su. Wannan ya kasance ne kamar yadda rundunar ta kuma bai wa jami'anta guda bakwai, wadanda suka yi fice a fagen ayyukansu kyautuka na kwarai.

Wannan karimcin, a cewar kwamishinan 'yan sanda (CP) Audu Madaki, shi ne karfafa jami'an rundunar su kara himma a bangarorinsu daban-daban na kokarin dakile ta'addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel