'Yan Ta'adda 131 Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda, An Kwato Makamai 785 a Benue

'Yan Ta'adda 131 Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda, An Kwato Makamai 785 a Benue

- Rundunar 'yan sanda cikin watanni uku sun samu nasarar kame 'yan ta'adda sama da 130 a Benue

- Rahoton ya ce an kwato makamai daban-daban sama da 780 a wasu sassan jihar ta Benue

- Hakazalika an dasa rundunonin 'yan sanda zuwa wasu yankuna masu hatsari na jihar ta Benue

Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Benue sun kama wasu mutane 131 da ake zargi da aikata laifi a fadin jihar. Ana zarginsu da aikata laifuka da suka hada da satar mutane, fashi da makami da kuma barna ta kungiyar asiri.

‘Yan sanda sun kuma kwato makamai daban-daban guda 785 daga hannun su.

Wannan ya kasance ne kamar yadda rundunar ta kuma bai wa jami'anta guda bakwai, wadanda suka yi fice a fagen ayyukansu kyautuka na kwarai.

Wannan karimcin, a cewar kwamishinan 'yan sanda (CP) Audu Madaki, shi ne karfafa jami'an rundunar su kara himma a bangarorinsu daban-daban na kokarin dakile ta'addanci a jihar.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma a Kaduna

'Yan Ta'adda 131 Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda, An Kwato Makamai 785
'Yan Ta'adda 131 Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda, An Kwato Makamai 785 Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Da yake gabatar da wasu daga cikin wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Màkurdi babban birnin jihar, CP ya ce daga watan Fabrairun 2021 zuwa yau, an kame masu aikata laifuka 205 a fadin jihar, an gurfanar da su a kotu kuma suna jiran hukunci.

“Tun lokacin da na fara aiki a ranar 22 ga watan Fabrairu zuwa yau, mun fara aiki mai karfi don wanke jihar daga aikata laifuka," in ji shi.

Madaki ya bayyana makaman da aka kwato cewa sun hada da bindigogi 32 kira daban-daban, AK-47 shida, G3 guda daya, wasu bindigogi biyu da kuma bindiga kirar gida guda 22.

Ya kara da cewa kananan bindigogin da ake kerawa a cikin gida sun fi yawa saboda yawancinsu makera ke yin su.

Ya kara da cewa, a yankin Sankara da ya zama wuraren da 'yan ta'adda suke, rundunar ta kafa wuraren aiki da tura jami'ai zuwa Katsina Ala, Gbor, Tor Donga, Abaji, da Anyiin don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, inji jaridar Punch.

KU KARANTA: Jami'an Kwastam Ta Kame Motar Dangote Makare da Haramtacciyar Shinkafar Waje

A bangare guda, Wani rahoton jaridar Aminiya ya nuna cewa ’yan bindiga sun kai farmaki garin Batsari da ke Jihar Katsina a karo na farko, inda suka kashe mutum guda sannan suka kuma yi garkuwa da wasu da dama.

Jaridar ta ruwaito cewa wani mazaunin ya yankin ya shaida mata a wayar tarho cewa mutumin da aka kashe ya kasance manomi mai suna Iliya Bakon-Zabo.

Ya ce: “Dazu, wata mata ta dawo, don haka ba za mu iya cewa ko duk wadanda suka bace suna hannunsu a yanzu ba ko a’a, amma a halin yanzu mun kirga mutum 27 da ba mu san inda suke ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel