Jami'an Kwastam Ta Kame Motar Dangote Makare da Haramtacciyar Shinkafar Waje
- Hukumar kwastam a Najeriya ta yi nasarar cafke wata motar Dangote makare da shinkafar waje
- Hukumar ta bayyana kame motar dauke da buhuna 600 na haramtacciyar shinkafar ta kasar waje
- Hakazalika a wani yankin hukumar ta kame kwayoyin tramadol da aka shigo dasu Najeriya a boye
Jami'an hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), sun ce sun kama wata babbar mota dauke da buhuna 600 na shinkafa 'yar kasar waje mai nauyin kilo 50.
Jami’an na NCS sun kuma cafke wasu mutane uku, ciki har da direban babbar motar, yayin da suke jigilar kayan zuwa yankin gabashin Najeriya.
Kwanturolan yanki na hukumar ta Kwastam, Peter Kolo, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a yayin ganawa da manema labarai na wata-wata kan ayyukan rundunar a Idiroko.
Kolo ya ce an tare motar ne a yankin kan iyakar Ijoun da ke jihar Ogun, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA: Ku Yi Hakuri: Kamfanin Rarraba Wutan Lantarkin Ya Nemi Gafarar 'Yan Jihar Kaduna
Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
Kwanturolan ya ce, a cikin watan Maris, rundunar ta tare wata babbar motar mallakar kamfanin kayan ababen sha na kwalba ta Najeriya da ake amfani da ita wajen shigo da kayayyaki ta haramtacciyar hanya zuwa cikin kasar.
A kan cafke haramtattun kayayyaki a cikin watan Afrilu, Kolo ya ce an kame buhuna 7,000 na shinkafa mai nauyin kilo 50 na kasar waje kwatankwacin kayan tirela 12.
Baya ga cafke haramtattun kayayyakin abinci, hukumar ta kama katan 1, 387 na kwayar Tramadol da aka boye a cikin katan dubu 1 na tayal a jihar Ribas.
Mrs Ifeoma Ojukwu, mai magana da yawun runduna ta II II dake tashar jirgin ruwa ta Onne a jihar Ribas, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Fatakwal, The Nation ta ruwaito.
Ojukwu ta ce an samu nasarar kwace kayayyakin ne tare da taimakon abokan huldar kasa da kasa.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma a Kaduna
A bangare guda, Jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC sun yi ram da yan damfarar yanar gizo wadanda aka fi sani da Yahoo-yahoo guda 34 a jihar Osun.
Daga cikin wadannan mutanen akwai jami'in Soja, Adebisi Jamiu, wanda ya gudu daga bakin aiki.
Hukumar ta damke wadannan matasa ne a simamen da ta kai da maraicen Talata, 18 ga Mayu, 2021 birnin Osogbo, jihar Osun.
Asali: Legit.ng