Ku Yi Hakuri: Kamfanin Rarraba Wutan Lantarkin Ya Nemi Gafarar 'Yan Jihar Kaduna

Ku Yi Hakuri: Kamfanin Rarraba Wutan Lantarkin Ya Nemi Gafarar 'Yan Jihar Kaduna

- Kamfanin rarraba wutan lantarki a jihar Kaduna ya ba kwastomominsa hakuri saboda rashin wuta

- Kamfanin ya bayyana cewa, lamarin ya fi karfinsa ne, amma ana kokarin shawo kan lamarin

- Kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Kaduna na ci gaba zazzafan musayar kalamai sakamakon yajin aiki

Kamfanin rarraba wutar lantarki a jihar Kaduna, Kaduna Electric ya sake bai wa abokan huldarsa hakuri game da rashin wuta a jihar tsawon kwana hudu sakamakon yajin aikin kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC).

A makon nan jihar Kaduna ta rikice da zanga-zanga biyo bayan korar wasu ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi, lamarin da ya tunzura dubban jama'a.

Kungiyar kwadago ta Najerita (NLC) ta tsundumawa yajin aiki sakamakon korar abokan aikinsu, lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon.

KU KARANTA: An Kuma: 'Yan Ta'adda Sun Bankawa Ofisoshin INEC Wuta a Jihar Ebonyi

Ku Yi Hakuri: Kamfanin Rarraba Wutan Lantarkin Ya Nemi Gafarar 'Yan Jihar Kaduna
Ku Yi Hakuri: Kamfanin Rarraba Wutan Lantarkin Ya Nemi Gafarar 'Yan Jihar Kaduna Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: UGC

Kamfanin rarraba wutan lantarkin na daga cikin ma'aikatun da suka tsunduma yajin aikin wanda ya jawo katse wutar lantarki a jihar tsawon kwanaki.

Kamfanin ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa: "Muna sane da irin haba-haba da kwastomominmu ke yi na ganin lantarki ta dawo, abin ya fi ƙarfinmu...Muna ba ku hakuri.

"Muna masu bakin cikin shaida muku cewa har yanzu ba a samu wani ci gaba ba game da sasanta rikicin da ya jawo daukewar wutar lantarkin a Jihar Kaduna."

Kamfanin ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar bangarorin biyu za su gaggauta sasantawa da juna domin ayyuka su ci gaba da gudana.

Shugaban kungiyar ta NLC, Ayuba Wabba da gwamnan jihar Nasir Ahmed El-Rufai na ci gaba musayar kalamai.

KU KARANTA: Kasar Saudiyya Za Ta Ba Afrika Tallafin Korona Har Dala Biliyan Daya

A wani labarin, Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ayuba Wabba, ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da yin hayar 'yan daba cike da manyan motoci 50 domin su fatattaki ma'aikata masu zanga-zanga a jihar.

Wabba ya bayyana hakan ne da safiyar ranar Laraba, 18 ga watan Mayu yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, a shirin Sunrise Daily.

Wabba ya zargin gwamnan jihar da biyan N500 ga kowane matashi domin kawo hargitsi a in da ma'aikata ke zanga-zangar korar adadi mai yawa na ma'aikatan gwamnati da jihar ta yi a ranar Talata, 18 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel