Kasar Saudiyya Za Ta Ba Afrika Tallafin Korona Har Dala Biliyan Daya

Kasar Saudiyya Za Ta Ba Afrika Tallafin Korona Har Dala Biliyan Daya

- Kasar Saudiyya ta amince da ba da tallafin bashin dala biliyan daya ga kasashen Afrika masu tasowa

- Kasar za ta ba da bashin ne ga kasashen da annobar korona ta yi fata-fata da tattalin arzikinsu

- Hakazalika kasar Saudiyya ta bayyana irin fannonin da ta sanya hannayen jari a wasu kasashen Afrika

Saudiyya za ta tallafa wa kasashen Afrika da hannun jari da bashi da adadinsu ya kai dala biliyan daya a wannan shekarar don farfado da tattalin arzikin su daga gibin da annobar korona ta bari, in ji Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ranar Talata.

"Asusun Saudiyya na Ci Gaba zai kaddamar da wasu ayyuka nan gaba, da bayar da bashi da kudinsu ya kai riyal biliyan uku ko kusan $1,000,000,000 a kasashe masu tasowa a Afrika cikin wannan shekarar," a cewar yariman a wani jawabi da ya yi a wani taro a birnin Paris.

Ya ce kuma ce kasarsa ta zuba kusan dala biliyan hudu a fannonin makamashi da hakar ma'adinai da sadarwa da abinci da sauran bangarori a Afrika kuma ya ce za ta ci gaba da duba wasu fannonin a wasu bangarorin nahiyar, BBC ta ruwaito.

KU KARANTA: Fashewar Gas Na Bogi Ya Kashe Mutane 2, Wasu Sun Jikkata a Wani Otal

Kasar Saudiyya Za Ta Ba 'Yan Afrika Tallafin Korona Har Dala Biliyan Daya
Kasar Saudiyya Za Ta Ba 'Yan Afrika Tallafin Korona Har Dala Biliyan Daya Hoto: timesofisrael.com
Asali: UGC

Shugabannin Afrika da sauran masu ruwa da tsaki sun gana a Paris ranar Talata don lalubo hanyoyin tallafa wa tattalin arzikin kasashen Afrika da annobar korona ta shafa da kuma tattauna basukan da nahiyar ke da su.

Taron G20 da Saudiyya ta karbi bakunci a shekarar da ta gabata ya bullo da dabaru don tallafawa tattalin arzikin Afirka yayin da SFD ta ba da rance ga kasashen na Afirka.

Hakazalika, jaridar Arab News ta ruwaito Yarima Mohammed yana cewa, kasarsa ta biya dala miliyan 122 don yaki da ta'addanci a gabar Afirka.

Yariman mai jiran gado ya ce "Muna fatan cewa wannan taron ya kammala tare da warware matsalolin da ke kan kasashen Afirka."

Ya kara da cewa, kasar Saudiyya ta bayar da lamuni da tallafi ga kasashen Afirka sama da 45.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

A wani labarin, Jihar Kaduna, musamman ma babban birninta ta ga mummunan yanayin kulle a ranar Litinin yayin da kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ke zanga-zangar korar ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi.

Akwai fargabar cewa, zanga-zangar ta shafi harkokin sufuri, kudade da bangarorin wutar lantarki wanda kan iya shafar tattalin arzikin jihar da ake ganin yana daga cikin manyan masu taka rawar gani a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar wani rahoton kididdiga da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) da ta fitar a shekarar 2019, ya zuwa shekarar 2017, Kaduna tana da wani Babban GDP na Naira tiriliyan 2.69 kuma itace matsayin na 10 a jerin jihohi masu karfin tattalin arziki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel