An Kuma: 'Yan Ta'adda Sun Bankawa Ofisoshin INEC Wuta a Jihar Ebonyi

An Kuma: 'Yan Ta'adda Sun Bankawa Ofisoshin INEC Wuta a Jihar Ebonyi

- Hukumar zabe ta INEC ta bada rahoton kone ofisoshinta biyu dake jihar Ebonyi jiya Talata

- An gano cewa, kone ofisoshin ya jawo asarar kayayyakin aiki da dama a cikin ofisoshin

- Rahoton ya bayyana cewa, babu asarar rai a yayin kone-kone, kuma ba a san wadanda suka yi ba

Wasu tsageru da ba asan ko su wanene ba sun bankawa ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) guda biyu wuta a jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Talata 18 ga watan Mayu, 2021 a ofishin INEC na birnin Ebonyi da na karamar hukumar Ezza ta arewa a jihar ta Ebonyi.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: An Dawo da £4.2m Zuwa Najeriya, Kudaden Da Ibori Ya Sace

An Kuma: 'Yan Ta'adda Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta a Jihar Ebonyi
An Kuma: 'Yan Ta'adda Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta a Jihar Ebonyi Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta gano wata sanarwa da hukumar ta INEC ta fitar da safiyar yau Laraba tana cewa:

"A daren jiya, Talata 18 ga Mayu 2021, wasu da ba a san ko su wanene ba sun kona ofisoshin INEC guda biyu a kananan hukumomin Ebonyi da Ezza ta Arewa na jihar Ebonyi. Babu asarar rai amma akwai lalacewa mai yawa ga gini da kayan aiki."

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

A wani labarin, Kasa da mako guda bayan fashewar gas a Abeokuta, wata fashewar ta sake faruwa a ranar Litinin a Abeokuta, jihar Ogun, inda mutane biyu suka mutu wasu uku suka ji rauni.

Lamarin wanda ya faru a otal mallakin tsohon gwamna Gbenga Daniel, an ruwaito cewa ya faru ne da misalin karfe 12 na dare lokacin da wani ma'aikaci ke cika wata kofa mai sarrafa kanta a kofar otal din.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa wani ma'aikaci da kuma daya da ake zaton yana daya daga cikin ma'aikatan sun mutu nan take, yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel