Hare-Haren Da Ake Kaiwa Ofisoshin INEC Zai Iya Shafar Zaɓe, Yakubu
- Farfesa Mahmood Yakubu shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC ya koka kan hare-haren da ake kaiwa hukumar
- Farfesa Yakubu ya ce harin na iya janyo cikas ga hukumar wurin gudanar da zabe yadda ya kamata
- Yakubu ya ce akwai alamar harin da gangan ake shirya shi don haka za su zauna da hukumomin tsaro game da batun
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce yawan hare-haren da aka kaiwa ofisoshin hukumar na iya kawo nakasu wurin gudanar da harkokin zabe a kasar kamar yadda hukumar ta wallafa
Yakubu, wanda ya koka game da hare-haren yayin taro da aka wallafa a shafinsu na Twitter ya ce, "a yanzu fa bisa dukkan alamu shiryawa aka yi domin a rika kaiwa INEC hari."
DUBA WANNAN: Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger
Ya nuna damuwarsa kan cewa hare-haren na iya shafar shirin da hukumar ta yi don yin zabe a kasar.
Binciken da The Nation ta yi ya nuna cewa kawo yanzu an kona ofisoshin hukumar INEC guda 23.
Kididdigan ya nuna cewa wuraren da abin ya fi sha sun hada da jihar Akwa Ibom (hudu), Abia (uku), Anambra (biyu) da Imo (biyu).
Sauran jihohin da aka samu gobara a ofisoshin INEC tsakanin watan Fabrairun 2019 zuwa Mayun 2021 sun hada da Borno, Ebonyi, Jigawa, Kano, Ondo, Plateau, Rivers da Abuja.
A sakon da ya wallafa a shafin Twitter na INEC @inecnigeria, Yakubu ya koka cewa kona musu ofisoshi da ake yi ya fara zama abin damuwa.
KU KARANTA: Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari
Yakubu ya ce hukumar za ta yi aiki da hukumomin tsaro domin ganin an magance matsalar kana ya bukaci mutanen da ofisoshin da ke garuruwansu su rika sa ido don ganin hakan ya dena faruwa.
Ya ce INEC za ta yi taro na musamman da hukumomin tsaro a ranar 24 ga watan Mayu.
A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.
An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.
Asali: Legit.ng